Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Benuwai ya tabbatar da cewa maharan suna ɗauke da Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya ce waɗanda suka aikata taɓargazar ranar 13 ga watan Yuni sun shiga jihar ne manyan makamai kuma ba tare da shanu.
Manhaja ta rawaito cewa sama da mutane 100 ne aka kashe a wani hari da aka kai garin Yelewata a ƙaramar hukumar Guma.
Shugaba Tinubu ya yi Alla-wadai da harin inda ya buƙaci shugabannin tsaro da su kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa a jihar Benuwai.
Wannan na zuwa ne bayan wata zanga-zangar kwana biyu da matasan jihar suka yi a jihar.
An soma zanga-zangar ne a ranar Asabar a kusa da babbar hanyar Lafia-Makurdi, sannan matasa sun yi tattaki zuwa babban birnin jihar Makurdi.
Manhaja ta kuma rawaito yadda ‘yan sanda suka harba barkonon tsohuwar kan masu zanga-zangar.
Shugaba Tinubu ya shirya kai ziyara jihar a ranar Laraba mai zuwa domin duba irin halin da ake ciki a cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin.
Tinubu dai ya gana da gwamnan jihar ta wayar tarho yana mai ba shi umarni kan bin matakan da aka tsara dauka tun da fari domin kawo karshen kashe-kashe a jihar.
Game da abin da gwamnan ya faɗa:
A wata hira da ya yi a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, gwamna Alia ya ce mahaifan waɗanda ake zargin Fulani ne sun shiga jihar ne da makamai samfurin AK-47 da AK-49.
Mista Alia ya ce, wasu daga cikin ‘yan ta’addan sukan shigo ne daga jihar Nassarawa ta iyakar ƙasar Kamaru.
Gwamnan ya ce maharan na ƙoƙarin kawo cikas ne g harkokin noma a jihar.
“A shekarar da ta gabata, mutane sun dawo garuruwansu domin su gudanar da aikin gona da fatan samun yabanya mai yawa,” ya faɗa.
Ya ce, “Sai dai yayin da ake shirye-shiryen noman bana, sai ga shi mun fara fuskantar sabbin hare-hare.”
Ya kuma ƙara da cewa, “salon hare-haren ya sauya. A baya muna magana ne a kan rikicin manoma da makiyaya. Amma yanzu abin ya fi haka, ana magana ne a kan makiyaya da ke shigowa da kuma wasu masu riƙe da makamai a cikinsu.”
“Muna kiransu makiyaya masu makamai. Abin da muke gani shi ne ba a shigo da shanu yanzu, sai wasu mutane da ke zuwa ɗauke suke da bindigi na AK-47 and AK-49.”
“Ba sa ma zuwa da shanu. Kuma mece ce manufarsu? Suna kai hari ne kuma bayan mako ɗaya sai wasu mutane su zo su zauna a wurin.
“Abin da muka fahimta shi ne, da ɗan gari a kan ci gari.”
“Abin da muka sani shi ne, makiyayan sun yi rikici, sai su makiyaya masu bindiga suka yi uwa suka makarɓiya, suka kuma rikiɗe zuwa ‘yan ta’adda.”
“Wannan ne halin da ake ciki yanzu.”
