CAF ta ƙwace kofin AFCON daga hannun Senegal ta bai wa Morocco

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar ƙwallon kafa ta Afirka (CAF) ta ƙwace kofin gasar AFCON na shekarar 2025 daga Senegal tare da bai wa Morocco nasara. Wannan hukunci ya biyo bayan rikicin da ya faru a wasan ƙarshe, inda ‘yan wasan Senegal suka bar fili na wani lokaci domin nuna rashin amincewa da hukuncin alƙalin wasa.

A cikin sanarwar da CAF ta fitar, ta bayyana cewa an soke sakamakon wasan da Senegal ta ci da ci 1-0, tare da mayar da shi 3-0 a hukumance a matsayin nasarar Morocco. Hukumar ta ce matakin ya biyo bayan saɓa dokokin wasa, musamman yadda aka dakatar da wasa na tsawon lokaci sakamakon zanga-zangar ‘yan wasa da magoya baya.

Rikicin ya samo asali ne bayan alƙalin wasa ya bai wa Morocco bugun fanareti a ƙarshen lokaci, lamarin da ya jawo fushin ‘yan wasan Senegal da magoya bayansu. Hakan ya kai ga dakatar da wasa na kusan mintuna 20, yayin da wasu magoya bayan Senegal suka yi yinƙurin shiga filin wasa tare da jefa abubuwa.

Duk da cewa an rasa bugun fanareti din, daga bisani Senegal ta zura ƙwallo a ƙarin lokaci ta hannun Pape Gueye, amma CAF ta yanke hukuncin cewa abubuwan da suka faru sun saɓa dokoki. Wannan ya sa aka ƙwace kofin daga Senegal tare da ayyana Morocco a matsayin zakaran gasar.

By ukarofi