Cire ni daga Sarkin Kano a 2020 bai firgita ni ba – Sarki Sunusi na ll

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana dalilin da ya sa ya kasance cikin natsuwa da jajircewa bayan rasa manyan mukaman da ya taba rike wa a rayuwar jama’a.

Sanusi ya yi wannan bayani ne yayin jawabinsa a taron Fola Adeola Annual Ramadan Lecture, inda ya yi magana kan muhimmancin juriya da imani da Allah wajen fuskantar sauye-sauyen rayuwa. Ya ce dogaro da Allah ne ya taimaka masa wajen tsallake mawuyacin lokaci bayan dakatar da shi daga muƙamin gwamnan CBN da kuma cire shi daga sarautar Kano.

Ya bayyana cewa mutane da dama kan yi kuskuren danganta iko da sakamako ga mutane, alhali a haƙiƙanin gaskiya komai yana canzawa ne bisa nufin Allah. A cewarsa, fahimtar cewa halin duniya ba ya dawwama yana taimaka wa mutum ya kasance mai haƙuri da hikima a cikin rayuwa.

Sarkin ya kuma gargaɗi mutane da su guji wulakanta kansu wajen neman yardar masu iko, yana mai cewa wasu na sunkuyar da kai ga mutane suna roƙo saboda suna zaton makomarsu tana hannunsu, alhali Allah ne ke ba da muƙami da ɗauke shi.

Da yake kawo misali da rayuwarsa, Sanusi ya ce sau da dama al’amura kan sauya cikin gaggawa. Ya ce an taɓa dakatar da shi daga muƙamin gwamnan CBN, amma bayan watanni uku kacal sai ya zama Sarkin Kano, lamarin da ya nuna yadda rayuwa ke sauyawa cikin ƙanƙanin lokaci.

Kazalika, ya ƙara da cewa bayan an cire shi daga sarauta a shekarar 2020, Allah ya sake dawo da shi kan karagar mulki bayan shekaru huɗu. A cewarsa, wannan ya ƙara tabbatar masa cewa komai yana hannun Allah, kuma mutum bai kamata ya firgita idan ya rasa muƙami ba.

Idan za’a iya tunawa dai an tuɓe Muhammadu Sanusi II daga sarautar Kano ne a shekarar 2020 a ƙarƙashin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, amma daga bisani aka mayar da shi kan karagar mulki a shekarar 2024 ta hannun gwamnan jihar Kano na yanzu, Abba Kabir Yusuf.

By ukarofi