
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF) ta fara shirye-shiryen ɗaukaka ƙara akan hukuncin FIFA na yin watsi da ƙorafinta akan Dimukraɗiyyar Jamhuriyar Kongo bisa rashin cancantar wasu ‘yan wasa da ƙasar ta yi amfani da su a wasanta da Nijeriya na neman gurbi a gasar Kofin Duniya na 2026, wanda aka gudanar a ranar 16 ga Nuwamban 2025 a Moroko.
Babban Sakataren NFF Dakta Muhammad Sanusi ya bayyana cewa, ba su gamsu da hukuncin hukumar ƙwallon ƙafar ta duniya ba, don haka suka fara yunƙurin ɗaukaka ƙara a kai.
A cikin ƙorafin, wanda aka shigar ‘yan kwanaki bayan wasan, an yi zargin rashin kiyaye dokoki daga Kongo wanda ya haɗa da bayar da fasfo ga ‘yan wasa da dama domin shigar sahun tawagar.
An tashin wasan ne 1 da 1 wanda ya sa aka kai zuwa zangon bugun fenariti, inda a nan ne Kongon ta yi nasara da ci 4 da 3 akan Super Eagles.
Ganin cewa FIFA ta yi watsi da ƙorafin Nijeriyar, NFF a yanzu tana ƙoƙarin ganin an sake nazari akan al’amarin ta hanyar ɗaukaka ƙara domin neman a soke hukuncin na farko da kuma samar da sabon sakamako a kai.
