CBN ya kammala shirin canjin kuɗi a yankunan karkara

Daga BASHIR ISAH

Babban Bankin Nijeriya, CBN, ya ce ya kammala shirin canjin tsoffin kuɗi da sabo a yankunan karkara da sauran yankunan da babu bankuna.

Muƙaddashin Kakakin CBN, Isa Abdulmumin, ne ya bayyana haka tare da cewa shirin ya cimma manufarsa.

A cewarsa, “Shirin ya kammala. Shirin abu ne mai ƙayyadadden lokaci amma ba wanda zai ci gaba da gudana ba.”

Sai dai Ƙungiyar Masu Hada-hadar Kuɗi ta Waya da Wakilan Bankuna a Nijeriya, ta bayyana shirin a matsayin mara armashi, saboda taƙaita damawa da masu ruwa da tsaki a cikinsa.

CBN ya ce an samar da shirin ne domin bai wa mazauna yankunan karkara da sauran wuraren da babu bankuna damar samun zarfin canja tsoffin kuɗinsu da sabo.

Domin cimman manufar shirin, shi ya sa aka tsame hannun masu POS da dangisu a Abuja da Legas domin bai wa kowa damar cin gajiyar shirin ko da babu asusun ajiya a banki, in ji CBN.

Babban Bankin ya ƙara da cewa, Naira 10,000 kacal kostoma zai iya samu a canja masa da sabon kuɗi yayin shirin.