Ceto ‘yan Kwara 176 alama ce ta Tinubu na samun nasarar yaƙi da ta’addanci, inji Iliyasu Kwankwaso

Spread the love

Bayan ceto mazauna al’ummomin Woro da Nuku guda 176 na Karamar Hukumar Kaiama a Jihar Kwara, wadanda aka sace a ranar 3 ga Fabrairu, suka sake samun ‘yanci, ya bayyana fili cewa Shugaba Tinubu na aiki tukuru domin ‘yantar da Kasar nan daga daurawar matsalolin rashin tsaro.

Wannan ceto da Sojojin Najeriya suka gudanar, ya kawo karshen kusan watanni shida na damuwa ga iyalansu da al’ummominsu.

Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin Jihar Kwara ta sanar da hakan a ranar Laraba ta shafinta na Facebook, inda ta bayyana ceton a matsayin babbar nasara. Ta kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, hukumomin tsaro da duk wanda ya ba da gudunmawa wajen gudanar da aikin.

Da yake tsokaci kan lamarin, Darakta na Kudi a Hukumar Kogin Hadejia Jama’are, Musa Illiyasu Kwankwaso, a cikin wata sanarwa ya ce ‘yan adawa a Najeriya su koyi yaba wa kokarin Gwamnati idan akwai nasara kan matsalolin tsaro da ke fuskantar Kasar.

Musa Illiyasu Kwankwaso, yayin da yake yaba wa Shugaba Tinubu, da Mai ba Shugaban Kasa shawara kan Harkokin Tsaro Nuhu Ribadu, da Ministocin Tsaro biyu da Shugabannin Rundunonin Sojoji, bisa wannan babban ceto na ‘yan Kwarawa 176 da aka sace, ya ce: “wannan hujja ce a fili cewa ba da dadewa ba tunanin rashin tsaro zai zama tarihi.”

Ya kara da cewa: “kokarin da Shugaba Tinubu ke yi wajen samar da tsaro a Kasar nan, mutanen Arewa musamman sun gane shi, kuma lallai za su nuna godiya da wannan karamci. Za su nuna wa kowa cewa yana da magoya baya na gaske wadanda za su kada masa kuri’a, ba wadanda ke kan Social media da gidajen Rediyo ba.”

“Magoya bayan Shugaba Tinubu a fili suke kuma ana iya kidaya su. Kowa zai ga yadda za su fito da yawa su kada wa Shugaban kuri’a, ba wadanda suke amfani da Social media wajen yada mummunan magana ba.”

By Babaji

Leave a Reply