Shugaban NASEPA ya nemi ƙarin ma’aikata tare da yabon Gwamna Sule

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Babban janar manaja na hukumar kula da tsabtace muhalli ta jihar Nasarawa da ake kira NASEPA Iliya Yusuf Adeka ya yi kira na musamman ga gwamnatin jihar da ta ɗauki ƙarin ma’aikata domin taimaka wa hukumar wajen magance yawan aikin da ke gabanta.

Iliya Yusuf Adeka ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da manema labarai a birnin Lafiya fadar gwamnatin jihar.

Adeka ya kuma  yaba wa gwamna Abdullahi Sule bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar ta hanyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa ta jihar akai-akai kawo yanzu.

Ya ƙara da cewa hukumar na cigaba da gudanar da kamfen na wayar da kan jama’a a sassa daban-daban na jihar domin wayar da kawunan mutane kan muhimmancin kiyaye tsaftar muhalli da guje wa ambaliya da sauran bala’o’in.

A cewarsa hukumar kan kai wannan gangamin wayar da kan al’umma baki ɗaya ne ga makarantu da kasuwanni da yankunan karkara da dai sauran su, kana ya kuma buƙaci jama’a da su guji toshe magudanan ruwa don ƙauracewa ambaliya kasancewar a yanzu damina yayi nisa.

Babban janar manaja ɗin ya ce hukumar na kuma wayar da kan jama’a kan illolin yin bahaya a waje maimakon tona bayan gida yana mai kira ga mutane da su gina bayan gida a gidajensu.

Ya ce yawan ambaliyar ruwa a jihar ya ragu sosai idan aka kwatanta da sauran jihohin ƙasar nan sakamakon wayar da kan da hukumar ke yi akai-akai kan wannan batu.

Daga ƙarshe sai Adeka ya yi amfani da damar inda ya yi kira na musamman ga al’ummar jihar baki ɗaya da su cigaba da bai wa hukumar haɗin kai domin tabbatar da tsaftataccen muhalli ga kowa.

By ukarofi

Leave a Reply