Charly Boy ya koka da yadda ’yan bindiga suka buƙaci miliyan N60 kan gawar Sarkin Gobir

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shahararren ɗan wasan kwaikwayo kuma mai fafutuka a Nijeriya, Charly Boy, ya nuna tayar da hankalin jama’a game da taɓarɓarewar tsaro a ƙasar, biyo bayan wani mummunan kisan da aka yi wa wani sarki bayan an kasa biyan kuɗin fansar sa.

A cikin jerin rubuce-rubucen da ya wallafa a shafinsa na ɗ, wato Tiwita, Charly Boy ya bayyana takaicinsa kan gazawar gwamnati wajen gano masu garkuwa da mutane, duk da kasancewar jami’an tsaro da sadarwa da dama.

A cewar Charly Boy, an yi garkuwa da Sarkin Gobir, inda masu garkuwa da mutane suka buƙaci a biya su kuɗin fansa naira biliyan ɗaya, inda aka gaza aiwatar da hakan, wanda ya yi sandin yi wa Sarkin kisan gilla.

Rahotanni sun bayyana cewa ɗan wanda aka kashe ya buƙaci a dawo da gawar mahaifinsa, sai dai masu garkuwa da mutane sun buƙaci ƙarin Naira miliyan 60 da babura shida a matsayin kuɗin fansa ga gawar.

Charly Boy ya soki gazawar jami’an tsaron ƙasar nan, inda ya nuna akwai hukumomi da dama kamar hukumar tsaro ta farin kaya (SSS), hukumar DSS, hukumar FIB, sashen binciken manyan laifuka CID, hukumar EFCC, Hukumar ICPC, da sojojin ƙasa, na ruwa da na sama.

Duk da kasancewar su, masu garkuwar sun ci gaba da cin karen su ba babbaka har da tattaunawa ta wayar tarho da iyalan Sarkin. 

Ya yi tambaya kan yadda masu garkuwan suka samu damar tattaunawa da dangin wanda aka kashe ta wayar tarho ba tare da an kama su ba.

By ukarofi