Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
A gurguje na taɓa bayyana tsarin farfagandar Hausa zalla da sak yanda ƙungiyar ‘yan awaren Biyafara IPOB ke kamfen ɗin wargaza Nijeriya ne. Don haka ma ‘yar uwar IPOB ta Arewa ta zama IPOH mai dauke da ‘yan kankambar soshiyal midiya masu hura wutar a kaure da yaki kawai. IPOB na kan gaba cikin waɗanda su ka dasa ‘yan karyar Hausa zalla don dinka rigar karya ta Hausawa su tada fitinar kabilanci a Arewa. Har yau ‘yan Hausa zalla sun kasa tabbatar da cewa su Hausawa ne hasalima a ɓoye su ke rufa wayar salula don sun san in sun fito za a gane ba su da wata hujja kuma maƙiya Hausawa da lamuran addini.
Jami’in rediyon Biyafara Chinasa Nworu na daga masu yayata ayyukan ‘yan ƙaryar Hausa zalla a duk lokacin da su ka murde wuyan tarihi don cimma burin kwangilar rusa Arewa da su ka ɗauko. Ga asalin ajandar IPOB ta hanyar makamashin kona Arewa/Hausa zalla da Nworu ya rubuta bayan wani mutumin kirki Bayarbe ya takale shi da ya daina haddasa fitina a tsakanin manyan ƙabilun Arewa. Ga fassarar nan “Arewa ta shirya domin babban muradin IPOB shi ne wargaza Nijeriya, sai kuma rarraba Arewa zuwa yankunan ƙabilu, kuma ko da mun dawo da Biyafara, ba za mu kyale su, su zama barazana a gare mu ba nan gaba,” inji Nworu.
Bayarben mai suna Balogun Arilaya ya yi wa Nwora hannunka mai sanda da cewa “Ka daina ƙarfafa ƙiyayya a tsakanin Hausawa da Fulani don sun kasance tare ba za a iya raba su ba. Bar su, su ci gaba da zamansu tare.”
Haƙiƙa IPOB na amfani da ‘yan ƙaryar Hausa zalla don wargaza Arewa don in Arewa na haɗe, ba yadda za a yi ‘yan IPOB su iya kafa Biyafara. Mun tuna yanda sojojin Nijeriya da manyan kwamandoji daga Arewa irin su Janar Murtala Muhammed, Janar Ibrahim Babangida, Janar Mamman Shuwa, Janar Hassan Katsina, Janar Yakubu Gowon, Janar Theophilus Danjuma, Janar Muhammadu Buhari da sauransu su ka yi kukan kura su ka dawo da Nijeriya ɗaya yayin da Odumegwu Ojukwu ya ayyana kafa Biyafara a 1967.
Sam kar mu ƙyale miyagun nan su cinnawa Arewa wuta don amfanin iyayen gidansu ‘yan IPOB. Kun tuna yanda su ka yi ta kamfen sai an sake Nnamdi Kanu duk da laifukan ta’addancin kashe-kashe da ya haddasa. Kun tuna yadda su ke ɗaukar maciyin amana Chukuma Nzeogwu a matsayin jan gwarzo duk da bindige Firimiya Sir Ahmadu Bello da matarsa Hajiya Hafsa da ya yi. Ta yaya ma waɗannan miyagun za su zama Hausawa? Na kara yi mu su ƙalubale da su fito fili za a gane ko su waye kuma don rashin kan gado ko sisin kobo ba za a saye su ba.
Tabbas saura kiris hukuma za ta fara cafke miyagun nan masu ingiza wutar yaƙin ƙabilanci, kuma ba wanda zai buya a salula da ba za a iya cafke shi ba don fuskantar tuhumar cin amanar ƙasa.
Duk wanda ya ɗauko tallar turmi zai gaji da yawo kafin sayar da ɗaya amma shi kuwa mai tallar totuwa ko ya gaji da yawo bai sha nauyin banza ba. Ma’ana masu iƙirarin Hausa zalla alhali ba Hausawa ba ne su na shan wahalar tilasta kan su kamantuwa da al’adun Hausawa don cimma burin kwangilar yaki da Hausawa su dira kan Musulunci da al’ummar da ta shafe shekaru aru-aru ta na zaune tare da juna lafiya ƙalau. Iyayen maƙiya zaman lafiya da ‘yan ƙaryar Hausa zalla ke kauna irin su Bishop Wilfred, Nnamdi Kanu, George Udom da sauran su kan iya bugun kirji su furzar da gubar da ke cikinsu don ba basaja sun fito a mutane. Mun gode wa Allah don yawanci ma gabanin mu haska ‘yan basaja, su kan fallasa kansu da kansu don ƙiyayyar ta su ta hana su zaman lafiya sakat yayin da yaƙin da su ke ingiza aukuwarsa tsakanin ‘yan Arewa ya ci tura. Kai an ƙi yin yaƙin sai kaka? Iye tahm.
Duk surutun da a ka yi ta yi kwanakin baya kan Amurka ta kawo hari Nijeriya biyo bayan bayanai na rashin sanin ya kamata da Bishop Wilfred daga jihar Binuwai ya kai sun kwanta dama ko hagu don shugaba Trump ba dan ƙaryar Hausa zalla ba ne don haka ‘yan kishin ƙasa sun ɗebo ruwa daga tekun atalantika sun watsawa guguwar kawo hari kan Nujeriya komai ya lafa waje ya yi tsit. Mugaye sun yi fatar a jefo bom kan jama’a a na tsakiyar sallar Jumma’a ko cin kasuwannin kauye. Haƙƙi ne kan kowane ɗan kasa ya marawa gwamnati da jami’an tsaro baya don tabbatar da zaman lafiya da murƙushe ‘yan ta’adda na daji da na soshiyal midiya. Sunan Bishop Wilfred ya mutu murus a kafafen sadarwa, gara ma Reɓerend Ezekiel Dachomo da ke ci gaba da cijewa kafin a ji tsit.
Wani abu da ke cikin ajandar ‘yan basaja shi ne rage ƙarfin siyasar Arewa da ke wanzuwa tun jamhuriya ta farko ta su Firimiya Sir Ahmadu Bello. Yin yarfe ga duk babban ɗan siyasar Arewa da cewa Bafulatani ne kaza da kaza gara ma Ojukwu ko mugun iri Nzeogwu da manyan ‘yan siyasar Arewa, duk surutun ya ki samun karbuwa don haka wasu mafiya kwaɗayi a cikin ‘yan basaja sun fara tallata wasu ‘yan takara da tunanin amfani da farafagandarsu don samun abun duniya. Marigayi shugaban siyasar kudu maso yamma Chief Obafemi Awolowo ne ya kirkiro Kalmar Hausa/Fulani don dabarar nuna ƙabilun biyu na mamaye harkokin mulki a Arewa don haka ƙananan ƙabilu su bijire. Fakewa da ƙaryar ƙabilanci, ba a addini kaɗai ba, a dimokraɗiyya ma haramun ne in an bi tanadin tsarin mulki. Duk mai son takara ga fili ga doki ya fito ya shiga jam’iyyar da ta kwanta ma sa a rai ya tallata kansa shikenan a gwabza a akwatin zabe. Zage-zage da cin zarafin wasu ‘yan siyasa ta doron ƙabilanci ko bambancin addini duk sun yi hannun riga da gaskiya kuma duk mai yin haka na kasadar fuskantar cafkewa daga jami’an tsaro bisa sabuwar dokar ba-sani-ba-sabo ta gwamnatin tarayya. Ai kowa ya ji jawabin shugaba Tinubu a lokacin gabatar da kasafin kuɗin 2026 gaban haɗin guiwar majalisar dokokin tarayya.
Duk mai gaskiya ba ya buya a wayar salula ya riƙa antayo guba. ‘Yan ƙaryar Hausa zalla yaran Ouba Ali Mohaman Tibati ku bayyana kanku in da gaske ku ke yi. Duk wanda ya buya ba sunan gaskiya ba hoto ya na maganar tada fitina mun san ɗan kwangila ne maƙiyin Hausawa, Musulunci da sauran al’ummar Arewa masu ƙaunar zaman lafiya.
Ina ma yadda Hausawan bogi ke aarfafa cin abincin Kirsimeti, haka su ke bin koyarwar BIBLE wajen yaƙi da tada fitina ciki da hana ƙabilanci. Mun ƙalubalance su da kawo hujjar ƙabilanci a BIBLE cikin littattafai 66 daga tsohon alƙawari littafin FARAWA har zuwa ƙarshen sabon alƙawari littafin RUYAR MANZANNI har yau tsit ka ke ji. Ashe dai sun jingine addinin koyarwar addini sun rungumi kwangilarsu ta rusa Arewa. Ai duk wanda ka ga addini bai gyara shi ba, ya yi wuf ya faɗa wata harkar; ka bincika ruwa baya tsami banza.
Duk murɗe wuyan tarihi da mutanen nan ke yi ba wata fa’ida da ta wuce kawo fitina a ƙasa mai ‘yanci kuma kowa na rayuwa da more ‘yancinsa bisa tanadin tsarin mulki. Nijeriya ai haɗaka a ka yi tsakanin Kudanci da Arewaci bisa doka ta mulkin gwamnatin tarayya a tsarin FEDARALIYYA. Duk mai korafi ya tafi kotu ya kai ƙara amma duk wanda ya hau soshiyal midiya ya na ruruta fitina kar ya ce an take ma sa ‘yanci idan an cafke shi.
Yau a sabon zamanin nan ba batun Daular Sokoto a ke yi ba ba Daular Benin ko Oyo ko Kanem Borno a Ngazargamu ko Kukawa a ke yi ba; a na magana a kan Tarayyar Nijeriya ƙarƙashin mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu ba Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ko shugaban ƙungiyar Kiristoci CAN Reɓerend Daniel Okoh ba. Jami’an tsaro ba za su ƙyale duk wani masu taka doka ɗan kwangila ya ci amanar ƙasa ya zauna a bayan wayar salula ya na dabdala ba. Haba ai ba ƙasar jahilai ba ce.
KAMMALAWA
’Yan ƙungiyar awaren Biyafara IPOB dai sun fito sun faɗi muradun da su ke son cimmawa da makamashin Hausawan bogi a Arewa. A wargaza Arewa zuwa garuruwan kabilanci, su kuma su kafa ƙasar Biyafara su yi ta rawar disko a Inugu ko Umuofia. Karyarsu ta sha karya. Wasu marar sa kishin Lardin Arewa da su ka ɗinka rigar Hausawa ; su sani ta yi mu su yawa su sauya wata dabarar don tayun wannan motor tada fitina sun fashe. A a Sarki Alwali a Burum-Burum ko Sarki Makau a masallacin idi ko jami’ar ‘Yandoto, duk wadannan labaru ba za su canja gaskiyar lamura ba, wanda ke da ƙorafi ko hujjar an cuci wani a tsohon zamanin zai iya tafiya kotu tun daga nan Nijeriya har kotun duniya a birnin Hague.
A ƙarshe mu na kira ga Sarki Reɓerend Shu’aibu Bargi ya yi amfani da wannan lokaci na bikin Kirsimeti wajen ja wa talakawansa kunne su gujewa biyewa IPOB don muradinsu shi ne cinna wutar yaƙi a Arewa kuma in wutar ta tashi hatta fadar Sarki Bargi ba za ta tsira ba.
DUK WANDA BAI JI BARI BA YA JI HOHO.
