Manufar ’yan ta’adda kan dawowar hare-hare a wuraren ibada

Spread the love

Daga Abba Abubakar Yakubu 

A yayin da al’ummar Musulmi ke gudanar da ibadar sallar Magariba a masallacin Jumma’a na Gomboru da ke birnin Maiduguri na Jihar Borno, a ranar Laraba da ta gabata, wanda ya zo daidai da lokacin da mabiya addinin Kirista a Gwoza da sauran sassan Nijeriya ke shirye-shiryen ƙarshe don gudanar da bikin Kirsimeti, kamar yadda suka saba duk shekara, domin tunawa da haihuwar Yeso Almasihu, wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bom ɗin dake ɗaure a jikinsa, wanda a take ya tarwatse ya kashe mutane aƙalla bakwai da jikkata wasu da dama.

Wannan yana zuwa ne a lokacin da za a ce ’yan Nijeriya sun fara mantawa da hare-hare irin waɗannan, waɗanda a shekarun baya, tun daga 2010 zuwa 2023, aka riƙa fuskanta a wuraren ibada daban-daban. Daga masallatai zuwa majami’u, kasuwanni da tashoshin mota, da mashaya, an hallaka rayuka da dama, hare-haren da ƙungiyar ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP suka riƙa ɗaukar alhakin kaiwa. A wani ɓangare na ƙoƙarin cusa tsoro da fargaba, da haifar da rikici tsakanin Musulmi da Kirista, da kuma nuna gazawar jami’an tsaron gwamnati, na daƙile ayyukan ta’addancin da suke yi.

Babu shakka a wancan lokacin ’yan Nijeriya sun samu kansu cikin wani mummunan yanayi na tsoro da rashin yarda da juna, da jifan juna da maganganu na tunzura jama’a, waɗanɗa suka ƙara tsananta matsalolin tsaron da aka riƙa fuskanta. Hatta a tsakanin shugabanni da ’yan siyasa da jami’an tsaro, an riƙa zargin juna da goyon bayan ta’addanci, da nuna ƙiyayya ga wani ɓangare. 

Bayan wasu shekaru, an samu sauye-sauye da dama, jami’an tsaro sun samu gagarumar nasara akan ƙungiyoyin ’yan ta’adda, duk da yake ba za a ce an kawar da matsalar tsaro gaba ɗaya ba, amma hare-haren bama-bamai sun ragu ko ma za a ce an dakatar da su. ’Yan Nijeriya sun fara sakin jiki da juna, an sassauta tsauraran matakan da aka riƙa ɗauka a wuraren ibada da na tarukan jama’a, saboda samun kwanciyar hankali. Hatta su kansu jami’an tsaro sun samu sauƙi da lafawar al’amura a ayyukan da suka riƙa yi na binciken ababen hawa a shingayen kan hanya, da samame da suke kaiwa maɓoyar ’yan ta’adda da sauran ayyukan samar da tsaro, a birane, ƙauyuka da kuma dazuka.

Sai dai bayan an samu ƙwarya-ƙwaryar zaman lafiya da inganta harkokin tsaro, a wasu wurare, sai gashi lamarin tsaro ya fara ɗaukar wani sabon salo, sakamakon ɓullar ƙungiyoyin ’yan bindiga dake satar mutane da dabbobi suna karɓar kuɗin fansa, da kuma kai hare-hare a ƙauyuka suna hallaka rayukan mata, tsofaffi, da ƙananan yara, da hana su zuwa gonaki ko ɗora musu mummunan haraji, kafin su girbe amfanin gonakin su.

Harin baya-bayan nan a masallacin Juma’a a Maiduguri ya tuna mana da harin da aka kai kan masu ibada a Babban Masallacin Jumma’a na Kano a shekarar 2014, wanda ya hallaka rayuka fiye da 120, da wasu ire-irensu a wasu masallatai, musamman a jihohin Borno, Yobe da Adamawa. Haka aka riƙa kai irin waɗannan hare-hare a majami’u da wuraren ibadar Kirista, musamman a lokacin bukukuwa Kirsimeti, a jihohin Filato, Kaduna, Borno, Neja, Ondo da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja. 

Nasan mai karatu ba zai manta da harin Ranar Kirsimeti da aka kai Majami’ar St Theresa’s Catholic Church dake Madallah a Abuja a shekarar 2011 ba, akwai kuma harin Majami’ar COCIN a Jos, Maiduguri da Damaturu, waɗanda rayuka da dama suka salwanta, aka sanya firgici, da damuwa a zukatan masu ibada da sauran ’yan Nijeriya. Kamar yadda na faɗa a baya manufar waɗannan ’yan ta’adda shi ne a ƙara raba kan ‘yan Nijeriya, a kunyata gwamnati da jami’an tsaro, ‘yan ta’adda su samu zarafin aiwatar da mummunan nufin su kan al’ummar ƙasa masu son zaman lafiya da cigaban rayuwarsu.

Harin ranar Laraba a Maiduguri, ya buɗe mana ido kan cewa hare-haren ’yan ta’adda ba su tafi gaba ɗaya ba, kuma ta’addanci na nan a kwance, lokaci ne kawai ’yan ta’adda ke jira, idan muka basu dama, da sakaci da rashin nuna kulawa, don su cigaba da abin da suka saba. Na yi imanin cewa da irin gogewa da jami’an tsaron mu suka samu kan ayyukan ’yan ta’adda, da sabbin kayan aiki na zamani da aka samu, da wayewar da ’yan Nijeriya suka samu daga abubuwan da suka riƙa faruwa na baya, ɓarnar da ’yan ta’adda suka yi mana a wancan lokacin ba za su sake maimaita irin ta ba.

Samun nasarar ’yan ta’adda a kanmu ya danganta ne da irin zaman kara zube da muke yi, rashin nuna kula da abubuwan dake faruwa a kewayen mu; raba kawunan mu da sunan addini ko ɓangaranci, rashin bai wa jami’an tsaro haɗin kai da rashin ba su bayanai masu muhimmanci da za su taimaka musu cimma nasara. Sannan idan muka ci gaba da bai wa ta’addanci gindin zama a tsakanin al’ummar mu, ba tare da fallasa mutanen da ake zargi da aikata ba daidai ba, ko ɓoye waɗanda hukuma ba ta yarda da su ba, haka kuma muka ci gaba da nuna goyon baya mutane su mallaki makamai da sunan kare kai. Waɗannan abubuwa sune suke bai wa rashin tsaro damar cigaba da mamaya, da ƙara wa ɓata-gari ƙarfi, da lalata zamantakewar mu.

Ina fatan za mu ci gaba da lura, muna ba da haɗin kai ga matakan tsaro, tare da tsananta addu’o’i a wuraren ibada. Kada mu manta mu dawo da tsare-tsaren mu na baya na matakan rigakafi kan tsaro, a dukkan wuraren mu na ibada, masallatai da coci-coci, har ma da kasuwanni da wuraren tarukan jama’a, kada a koma a naɗe hannu. Allah ubangiji ya taimake mu kan maƙiya zaman lafiya, amin.

Da fatan za mu shiga cikin sabuwar shekarar 2026 cikin masu rai da lafiya

By ukarofi