
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Cibiyar ‘Wadata Media and Advocacy Centre’ (WAMAC) ta bayyana damuwa akan kamawa da tsare ɗan jaridar kare ‘yancin al’umma da kuma binciken ƙwaf, Ahmed Isa Sakpe a Minna, Jihar Neja.
WAMAC ta ce, babban jami’in gwamnatin Gwamna Umaru Bago, wato B. Y. Daban ne ya umarci rundunar ‘yan sanda jihar da su kama ɗan jaridar bisa tuhumar sa da laifin cin fuska ta yanar gizo a daidai lokacin da yake kan aikinsa.
A cewarta, wannan al’amari ya nuna yadda gwamnatin Bago ta ke ƙin biyayya ga dokokin ‘yancin yaɗa labarai da kuma amfani da ƙarfin gwamnati wajen cin mutunci da wulaƙanta ‘yan jarida.
A sanarwar da jami’arta na hulɗa da jama’a, Nonye Maria Aghaji ta fitar, WAMAC ta ce, waɗannan al’amura daga jami’in da ‘yan sanda wulaƙanta mulki ne da ƙoƙarin hana jin bakin al’umma wajen bayyana kokensu ga harkokin gwamnati.
WAMAC ta bayyana hakan a matsayin wani nau’i na musguna wa aikin jaridar binciken ƙwaf da rufe bakin ‘yan adawa a jihar, tana mai cewa ire-iren matsin ya samo asali ne daga mulkin soji, inda ake wulaƙanta ‘yan jarida saboda faɗin gaskiya akan gwamnati.
Akan haka cibiyar ta tunatar da lokacin da Cibiyar Harkokin Jarida ta Ƙasa-da-ƙasa (IPI) ta sanya Gwamna Bago da gwamnatin Neja a sahun waɗanda ake da damuwa akansu bisa irin aikin.
A ƙarshe, ta yi kira da a gaggauta sako Isa Sakpe da a kawo ƙarshen irin wannan wulaƙancin da ake yi wa ‘yan jarida a jihar.
