Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano na sanar da ɗaukacin masu gudanar da gidajen wasanni a faɗin jihar wato gidajen gala da masu sana’ar sauti ta (DJ) cewa, daga ranar Laraba 18 ga Fabrairu, 2026, Hukumar ta rufe dukkan gidajen wasanninsu har zuwa ƙarshen watan Ramadan, wannan doka za ta fara aiki ne da misalin ƙarfe goma na dare.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Manhaja.
Hukumar ta ɗauki wannan mataki ne domin ba da damar gudanar da ibada cikin nutsuwa a yayin azumin watan Ramadan mai alfarma. A cewar ta rufe gidajen wasannin zai ci gaba har zuwa lokacin da za a kammala azumin watan Ramadan tare da saurarar lokacin buɗe su a yayin bukukuwan Sallah, wanda hukumar za ta sanar da zarar lokaci ya yi.
Hukumar na kira ga duk masu ruwa da tsaki da su bada cikakken haɗin kai tare da bin wannan umarni kamar yadda doka ta tanada. Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin hukumar na tabbatar da ana bin dokar da ta kafa.
Daga nan hukumar na addu’ar Allah yasa a gudanar da ibadu cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali, Ya kuma maimaita mana watan cikin rahama da albarka.
