Cikakken sunayen jami’an da Ministan Cikin Gida ya dakatar kan mutuwar masu haƙar ma’adinai 37 a Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya umarci a dakatar da jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC) guda 20 bisa zargin su da hannu a mutuwar masu haƙar ma’adinai 37 ba bisa ƙa’ida ba a ofishin NSCDC a Jihar Neja, har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

Wannan na zuwa ne bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike mai cike da adalci kan al’amarin, wanda ya auku a ranar Alhamis.

A cewar wata sanarwa da mai ɗauke da sanya hannun ministan, jami’an sune: ” the O/C Station Guard, SC Usman Isah Ndamaka; Station Guard, ASCI Hassan Mohammed; Station Guard, CCA Bala Mohammed; Arresting Officer/O/C Investigation, CSC Oluwadare Sunday; Arresting Officer, DCC Obafemi Elvis; Arresting Officer, CSC Annas Shitto Lamino; HOD INT/INV, DCC Philip Ajayi; O/C Legal, ACC Barr. Stephen Tsado; Day/Night Duty Officer, ASCI Alhassan Mohammed; and Guard Duty, IC Abdullahi Sale.”

Sauran sun haɗa da: “Guard Duty, IC Mohammed Sonfada; Guard Duty, CAI Liman Abubakar; Guard Duty, CAI Bala Usman; Guard Duty, IC Mohammed Jiya; Guard Duty, DSC Isah Suleiman; Guard Duty, CAI Ahmed Wushishi; Guard Duty, IC Sale Adamu; Guard Duty, IC Haruna Mohammed; Guard Duty, ASCI Aliyu Sallah; and Guard Duty, CAI Isah Sanusi”, kamar yadda jaridar NewsPointNigeria ta wallafa.

Sannan, Tunji-Ojo ya kafa kwamiti mai zaman kansa na mutane 10 domin gudanar da bincike kan mutuwar masu haƙar ma’adinan da aka ce an kama su ne bisa aiki ba bisa doka ba.

Ya kuma koka kan faruwar al’amarin inda ya ce gwamnati na ƙoƙarin sauke nauyin da ke kanta a kai wajen tabbatar da adalci. Ana sa ran kwamitin zai binciko ainihin sunayen mamatan da gudanar da bincike kan kame, tsarewa da dalilan da suka sabbaba mutuwarsu.

Mambobin kwamitin sun haɗa da:

“Mr Jonathan Kure, mni — retired Deputy Director-General, Department of State Services — Chairman Prof. Isa Hayatu Chiroma (SAN) — former Director-General of the Nigeria Law School — Secretary
AIG Hosea Hassan Karma (retired)
Prof. Olayinka Buhari — Professor of Histopathology and former Chief Medical Director of the University of Ilorin Teaching Hospital
Representative of the Minna Emirate Council
Representative of the Niger State Government
Alhaji Liman Sulaiman — National Secretary, Miners Association of Nigeria
Mr Deji Adeyanju — lawyer and human rights activist
Mrs Zainab Suleiman Okino — Blueprint Newspaper
Dr George Agbakahi — Public Affairs Analyst”, kamar yadda jaridar ta wallafa.

A ƙarshe, Ministan ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da kuma kira a gare su da su kwantar da hankali yayin da ake cigaba da gudanar da bincike akan lamarin.

By Babaji

Leave a Reply