Cin Zarafi: Sarakunan Nafada da Funakaye sun goyi bayan dokar VAPP

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

A ci gaba da ƙoƙarin daƙile cin zarafin mata da yara a Gombe, ma’aikatar mata da Walwalar Jama’a ƙarƙashin jagorancin Kwamishiniya Asma’u Muhammad Iganus ta kai ziyara masarautun Nafada da Funakaye, domin ƙaddamar da kwamitocin yaƙi da cin zarafi a yankunan.

A yayin ziyarar farko zuwa Masarautar Nafada, Kwamishiniyar ta bayyana damuwarta kan alƙaluman da suka nuna cewa Gombe na fama da matsalar cin zarafi da kashi 87.46%, abin da ta bayyana a matsayin barazana ga zaman lafiya da ci gaban al’umma. Ta ce hakan ne ya sa ake kai ziyara domin jan hankalin sarakunan gargajiya su shiga tsaka-tsakin yaƙi da lamarin.

Da yake jawabi, Sarkin Nafada, Alhaji Muhammad Dadum Hamza, ya nuna takaicinsa kan yadda fyaɗe da cin zarafi ke ƙaruwa, yana mai tabbatar da cewa:
“A Nafada babu mafaka ga mai laifin fyaɗe. Zan tsaya da kaina wajen ganin an hukunta duk wanda aka samu da laifi.”

Ya kuma bayyana mamakinsa kan yadda yaran Gombe ba su fitowa kan gaba a jarabawar WAEC da NECO, amma suna kan gaba a rahotannin cin zarafi. Ya ce yana goyon bayan hukuncin ɗaurin rai da rai, maimakon hukuncin shekaru 14 da ake dasawa yanzu.

Daga nan tawagar ta wuce Masarautar Funakaye, inda Sarkin Funakaye, Alhaji Yakubu Muhammad Kwairanga IV, ya nuna cikakken goyon bayansa ga matakin gwamnati kan yaki da cin zarafi. Ya ce ba dole bane a nuna sassauci ga masu aikata irin wannan mummunan laifi, domin hakan ne kawai zai daƙile yawan faruwarsa.

A nasa jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Funakaye, Alhaji Abdurrahman Shua’ibu Adam, ya ce suna tare da duk wani mataki da gwamnati take ɗauka na kare rayuwar mata da yara. Ya jinjinawa Kwamishiniyar Mata bisa jajircewarta wajen tunkarar matsalar da ta kai jihar ga kaso 87.46%.

A ƙarshe, Kwamishiniyar ta miƙa kundin Dokar VAPP ga Masarautar Funakaye domin fara cikakken aiwatar da aikin kwamitin a yankin.

By ukarofi