Yara miliyan 2.8 za a yiwa rigakafin Polio a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Tuni dai Gwamnati ta tura ma’aikata 3,700, ciki har da ƙungiyoyin masu zagayen gida-gida su 961, an kuma tanadi fiye da allurai miliyan 2 domin gudanar da allurar rigafin.

Haka kuma akwai ƙungiyoyi na musamman su 993 da za su riƙa aiki a kasuwanni, tashoshin mota, tituna da wuraren cunkoso.

Wakilin UNICEF na yankin Kano, R. M. Farah, shi ne ya bayyana haka a yayin da yake ganawa da manema labarai a Katsina.

A cewar Malam Farah, UNICEF na ci gaba da haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai saboda rawar da suke takawa wajen tabbatar da cewa kowane yaro ya samu rigakafin.

Ya kuma jaddada muhimmancin gidajen rediyo wajen isar da sako ga yankunan da ke da nisa da cibiyoyin sadarwa.

Ita kuwa hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta buƙaci kafafen yaɗa labarai, musamman gidajen rediyo, da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kai kafin gudanar da sabon yaƙin rigakafin cutar shan-inna (Polio) a faɗin Jihar Katsina.

Haka kuma wakilin UNICEF ya yabawa Jihar Katsina bisa nasarar da ta samu na rage yaɗuwar cutar Polio da kusan kashi 80 cikin 100 daga 2024 zuwa 2025, wanda ya bayyana cewa wannan babban nasara ce da kuma ci gaba.

Sai dai ya gargaɗi cewa, cutar Polio ba ta da iyaka, don haka duk da raguwar, kowace jiha na cikin haɗari muddin an samu ko guda ɗaya yana yawo a ƙasar.

Farah ya ce, wajibi ne a kai aƙalla kashi 95 cikin 100 na yawan yaran da ake buƙatar yi wa rigakafi domin daƙile yaɗuwar cutar gaba ɗaya.

Tuni dai, UNICEF ta jaddada cewa, rigakafin cikin gida na nan kullum a cibiyoyin lafiya, ba wai lokacin kamfen kaɗai ake yi ba, inda ya jaddada cewa, sun haɗa kai da cibiyoyin kiwon lafiya na yau da kullum a cikin wannan kamfen domin tabbatar da bada kulawa kan ayyukan.

Kazalika, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Katsina da abokan hulɗa bisa jajircewar su, sannan ya buƙaci kafafen yaɗa labarai, kan gudummuwar da suke ba su a koda yaushe.

By ukarofi