CSACEFA ta yi jimamin rasuwar yara biyar a haɗarin mota a Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Ƙungiyar ƙungiyoyin farar hula masu yaƙi da jahilci da bunƙasa Ilimi (CSACEFA) ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan Malam Mansir Adamu, sakamakon rasuwar ’ya’yansa guda biyar a wani haɗarin mota da ya faru a cikin birnin Gombe.

Yaran sun rasu ne a ranar Talata, bayan da tankar ruwa ta yi karo da keken adaidaita sahu da ke ɗauke da su a yankin unguwar Federal Low-Cost da ke cikin birnin Gombe, babban birnin jihar.

A cikin saƙon ta’aziyyar, ƙungiyar, ta hannun wakiliyar ta, Halima Ahmad Mahdi, ta bayyana lamarin a matsayin babban bala’i da ya katse rayuwar ƙananan yara biyar masu kyakkyawar makoma.

Ta ce rasuwar yaran ta jefa iyalansu, ’yan uwansu da sauran al’ummar yankin cikin alhini da jimami, tare da miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyayen yaran bisa wannan babban rashi mai raɗaɗi.

Mahdi ta kuma jajanta wa shugabanci da ma’aikatan makarantun da yaran ke zuwa, da abokan karatunsu, da kuma al’ummar Jekadafari, tana mai cewa wannan rashi ya shafi al’umma baki ɗaya, ba iyalan yaran kaɗai ba.

Haka kuma, ta yi addu’ar Allah ya ba sauran yaran da suka jikkata a haɗarin lafiya cikin gaggawa, ya warkar da su, ya kuma ƙarfafa musu gwiwa.

Ta ce: “Muna roƙon Allah maɗaukakin sarki ya gafarta wa yaran da suka rasu kurakuransu, ya sanya su a Aljannatul Firdaus, ya kuma ba iyayensu da sauran iyalansu ƙarfin zuciya, haƙuri da juriya wajen jure wannan babban rashi da ba ya da musaltuwa.”

Wakiliyar CSACEFA ta kuma yi addu’ar Allah ya sanyaya zukatan iyalan da abin ya shafa, tare da kira ga al’umma da su riƙa yi wa mamatan addu’a da kuma sauran waɗanda wannan bala’i ya shafa.

Ta ƙara da kira ga jama’a da su riƙa addu’ar Allah ya kare yara da sauran masu amfani da hanyoyi daga afkuwar irin waɗannan haɗurra, tana mai jaddada muhimmancin neman taimakon Allah domin kauce wa sake salwantar da rayukan waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Wannan mummunan lamari ya jefa iyalan mamatan da al’ummar yankin cikin alhini bisa rasuwar yaran biyar.

By ukarofi

Leave a Reply