Daga USMAN KAROFI
Hukumar yaƙi sa cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa cutar sanƙarau na ƙara ƙamari a jihohin Arewacin ƙasar, inda masana kiwon lafiya ke gargaɗin cewa alluran rigakafin da ake da su a yanzu ba sa bayar da cikakkiyar kariya ga nau’in cutar serogroup C da ke yaɗuwa cikin sauri.
Rahotanni sun nuna cewa yara masu shekaru daga ɗaya zuwa 15 su ne suka fi kamuwa da cutar, yayin da cunkoson jama’a da iska mai ɗauke da ƙura a lokacin rani ke ƙara haɗarin yaɗuwar cutar a yankunan da ke cikin meningitis belt na Afirka.
Babban daraktan NCDC, Dakta Jide Idris, ya bayyana haka a wani taron kwamitin kula da Asusun Kiwon Lafiya na Ƙasa (BHCPF) a Abuja. Ya ce duk da muhimmancin rigakafi, akwai buƙatar ƙarin matakai domin shawo kan cutar, musamman ganin cewa nau’in cutar da ke yaɗuwa ba ya dacewa sosai da alluran da ake da su.
Ya ƙara da cewa cutar sanƙarau na yaɗuwa ne ta hanyar numfashi, musamman a wuraren da ke da cunkoso ko rashin iska mai kyau, kuma na iya kashe mutum cikin sa’o’i kaɗan idan ba a gano ta da wuri ba. Ya jaddada muhimmancin gano cutar da wuri da kuma ba da magani cikin gaggawa domin rage mace-mace da illolinta.
