Tinubu zai tafi Umara a gobe Alhamis

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Alhamis, 29 ga Oktoba, 2026 ake sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Birnin Tarayya Abuja domin zuwa ƙasar Saudiyya, inda zai gudanar da ibadar Umara kuma ya yi wa Nijeriya addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da ɗorewar al’amura.

Tinubu zai kama hanyar tafiyar ne bayan ya halarci taron ƙaddamar da makaman da Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) ta mallaka a Sashen Shugaban Ƙasa na Filin Jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

A cewar sanarwar da Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya fitar a yau Laraba, ya ce Tinubu zai yi amfani da bulaguron nasa ne wajen yin addu’ar samun taimako da albarkar ubangiji ga Nijeriya. “Yayin kasancewarsa a Makka, Shugaba Tinubu zai gudanar da ibada mai alaƙa da Umara wajen neman taimako da albarkar Allah ga Nijeriya da al’ummarta,” inji sanarwar.

By Babaji

Leave a Reply