Da Ɗumi-Ɗumi: Arsenal ta lashe Premier League bayan jiran shekaru 22

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta yi nasarar lashe kofin gasar Premier League na ƙasar Ingila bayan shekaru 22 tana dako.

Hakan na zuwa ne bayan da Manchester City da ke biye mata a teburin ta ɓara da maki a karawa ta da ƙungiyar Bournemouth a wasa na 37 a gasar.

Wannan na nufin Arsenal da ke da maki 82 ta lashe kofin yayin da ya rage saura wasa ɗaya a kakar ta 2025/2026.

Ita kuwa City a yanzu tana da maki 78 bayan tashi 1 da 1 a wasan yau, wanda ke nuna ba za ta samu adadin maki kamar Arsenal ɗin ba a wannan kakar.

By Babaji