
Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE
Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya janye daga takarar gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Pantami, wanda tun farko ya nuna rashin amincewa da tsarin maslaha da jam’iyyar ta yi wanda ya bai wa Jamilu Gwamna tikitin takara, ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
A wata sanarwa da Barrista Ibrahim M. Attahir ya fitar a madadin ƙungiyar Pantamiyya Movement, Pantami ya zargi shugabannin jam’iyyar da rashin tabbatar da sahihin tsarin gudanar da zaɓen fidda gwani.
Sanarwar ta ce an hana Pantami samun muhimman bayanai kan yadda za a gudanar da zaɓen kai tsaye, ciki har da tsarin tantance masu kaɗa ƙuri’a, wuraren tattara sakamako da kuma yadda za a gudanar da zaɓen gaba ɗaya.
“Wasiƙun da lauyoyinsa suka aika wa sassan jam’iyyar domin neman ƙarin bayani ba a amsa musu ba, kuma har yanzu ba a warware matsalolin da aka gabatar ba,” in ji sanarwar.
Pantami ya kuma yi zargin cewa an karya dokar zaɓe ta 2026 da kuma ƙa’idojin jam’iyyar APC wajen shirya zaɓen fidda gwani a jihar.
Ya ce abin da ya faru a zaɓen fidda gwani na ’yan majalisar tarayya da aka gudanar a kwanakin baya ya nuna cewa an ware mambobin jam’iyya na ƙasa daga tsarin zaɓen.
A cewar sanarwar, ƙarfin Pantami yana kan dimbin goyon bayan da yake samu daga matasa da mata a faɗin jihar Gombe.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Pantami ne kaɗai daga cikin ’yan takarar gwamna da ya aika wakili wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Rundunar ’Yan Sanda ta shirya a Gombe ranar 14 ga watan Mayu.
“Bayan nazari mai zurfi da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, Farfesa Pantami ya yanke shawarar janyewa daga zaɓen fidda gwani na gwamna da za a gudanar ranar 21 ga Mayu, 2026, a matsayin nuna rashin amincewa,” sanarwar ta ƙara da cewa.
Pantami ya gode wa matasa da suka tara kuɗin sayen fom ɗinsa, tare da yaba wa magoya bayansa musamman mata da matasa bisa goyon bayan da suka nuna masa.
Haka kuma ya buƙaci mabiyansa da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Gombe.
Sanarwar ta ce ƙungiyar Pantamiyya Movement za ta sanar da mataki na gaba da shirinta nan gaba.
