Ƙungiyar APC Concern Group a Nasarawa ta nuna ɓacin rai kan yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani

Spread the love

Daga JOHN WADA a Lafia

Ƙungiyar All Progressives Congress (APC) concern group a jihar Nasarawa ta nuna ɓacin rai kan yadda aka gudanar da zaɓukan fidda gwanin jam’iyyar da aka gudanar a faɗin jihar a yanzu inda suka bayyana tsarin a matsayin zamba.

A cewar ƙungiyar dukkan tsarin zaɓen da aka gudanar a jihar kawo yanzu ya cika da maguɗi kuma bai bi ƙa’idar dimokuraɗiyya da adalci ba.

Da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar ƙungiyar ‘yan jaridu na jihar Nasarawa dake Lafia babban birnin jihar shugaban tawagar honorabul Abdullahi Yammani ya bayyana cewa an tsara zaɓukan da gangan domin amfanar da wasu ‘yan takara yana mai cewa an hana magoya baya da masu biyayya ga jam’iyyar damar kaɗa ƙuri’a cikin ‘yanci.

A cewarsa ya zagaya wasu mazaɓu a ranar zaɓen domin lura da yadda ake gudanar da tsarin da idanunsa amma abin da ya gani abun takaici ne kuma abun kunya.

Ya cigaba da bayyana cewa “ Mun zagaya mazaɓu daban-daban domin ganin abin da ke faruwa da kanmu. Abin da muka gani ya nuna a sarari cewa an riga an tsara tsarin,” in ji shi.

Honorabul Abdullahi Yammani ya ƙara zargin cewa magoya bayan jam’iyyar ta APC a jihar da dama ba su iya kaɗa ƙuri’a ba saboda takunkumin tsaro da ruɗani da aka samu a wuraren zaɓen daban-daban. Ya kuma ce a wasu yankuna ma tashin hankali ya kawo cikas ga zaɓen bayan ‘yan daba sun mamaye wuraren kaɗa ƙuri’a.

Ya gargaɗi cewa irin wannan lamari zai iya sa masu kishin jam’iyyar su yi nisa kuma ya raunata haɗin kan APC idan ba a magance shi yadda ya dace ba.

“Idan APC ta cigaba haka masu son jam’iyyar da yawa za su iya barin ta domin babu ƙarfafa wa ko adalci ga mambobin da suka sadaukar,” in ji shi.

Yammani ya ƙara zargin cewa yayin da zaɓen ke cigaba a wasu mazaɓu ya samu labarin cewa an riga an tattara sakamako kuma aka miƙa shi ba tare da wakilan sa ba.

Ko da yake ya nuna rashin jin daɗinsa kan tsarin ya ce za su cigaba da natsuwa ya kuma nazarci lamarin kafin ya yanke shawarar matakin da za su ɗauka ta tsarin dokokin jam’iyyar inda ya kuma yi amfani da damar ya yi kira na musamman ga shugaban jami’iyyar APC na ƙasa ya sa baki a lamarin cikin gaggawa kafin hakan ya shafi jam’iyyar a zaɓukan gama-gari na 2027 da ke tafe.

“Zamu bi ƙa’ida. Ba zamu nemi gajeriyar hanya ba amma zamu jira mu gani abin da jam’iyyar za ta yi,” in ji shi.

By ukarofi