
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas ya sanar da komawarsa zuwa jam’iyyar APC.
Fubara ya bayyana haka ne yayin wani zama na masu ruwa tsaki a gidan Gwamnatin jihar.
Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan ya fice daga babbar jam’iyyar adawa PDP.
Idan ba a manta ba a jiya Litinin ne gwamnan ya yi wata ganawar sirri da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
