
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun 6 da 9 ga watan Yuni, 2025 a matsayin lokutan hutu domin gudanar da hidimar Eid-ul-Adha, wato babbar Salla.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana hakan a madadinta, inda ya kuma taya ɗaukacin al’ummar musulmi a gida da waje murnar zagayowar lokacin.
A sanarwar da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dakta Magdalene Ajani ta fitar, Ministan ya yi kira ga al’ummar musulmi da su cigaba da bin karantarwar addinin wajen sadaukarwa da tsayuwa akan imani musamman a koyi da Annabi Ibrahim (AS) da kuma amfani da lokacin wajen yi wa Nijeriya addu’ar samun zaman lafiya da ci-gaba.
Ministan ya kuma tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa gyare-gyare da shirye-shiryen da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yi a ƙarƙashin shirin Sabunta Ƙasa, ana yin su ne don dawo martabarta ne da ɗora ta akan hanyoyin ci-gaba.
Ya kuma yi fatan yin hidimar cikin lumana da kwanciyar hankali tare da kira ga sauran al’ummar ƙasa wajen haɗa hannu da gwamnati a ƙoƙarinta na ciyar da ƙasar gaba.
