Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnatin Tarayya na ganawa da Ƙungiyar Ƙwadago

Spread the love

A ƙoƙarin da take yi don hana Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago shiga yajin aikin da ta ƙudiri aniya, Gwamnatin Tarayya na can tana tattaunawa da shugabannin ƙungiyar a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja da yammacin wannan Asabar.

Ya zuwa haɗa wannan labarin, majiyarmu ta ce an hango wasu fitattun jagororin ƙungiyar na shiga wurin taron, ciki har da Shugaban NLC na Ƙasa, Joe Ajaero da Sakataren Ƙungiyar na Ƙasa, Emma Ugboaja da Babban Sakataren TUC, Nuhu Toro da sauransu.

Wakilan gwamnati a wajen taron sun haɗa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajiabiamila, ministocin ƙwadago, Simon Lalong da Nkeiruka Onyejoecha, da dai sauransu.

Idan za a iya tunawa, NLC da TUC sun yi barazanar shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani daga ranar 3 ga Oktoban 2023, sakamakon gazawar gwamnati wajen cimma buƙatunsu biyo bayan cire tallafin mai.

By Editor