Buhari ya taya ‘yan Nijeriya murnar zagayowar Ranar Samun ‘Yancin Kai

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya taya ɗaukacin ‘yan Nijeriya murnar zagayowar Ranar Samun ‘Yancin Kai.

Kazalika, Buhari ya taya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu murnar cikar Nijeriya shekara 63 da samun ‘yan cin kai.

“A dai dai lokacin da ƙasar nan ke bikin samun ‘yan kai, ina miƙa jinjinata ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da al’umar Nijeriya,” inji shi.

Buhari ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar.

“Tsawon shekaru 63, Nijeriya na ci gaba da zaburar da sauran ƙasashen nahiyar Afrika ta hanyar ƙirƙire-ƙirƙire da kuma ɗorewar mulkin dimokuraɗiyya,” in ji Buhari.

A cewar tsohon shugaban ƙasar yana da ƙwarin gwiwar cewa dimokaraɗiyya a matsayin tsarin gwamnati, za ta ci gaba da samun karfi shekaru masu zuwa a ƙasar nan.

By Editor