Jawabin mai girma, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCRFR, kuma Babban Kwamandan Askarawan Nijeriya a cikar Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya shekaru 63 da samun ‘yancin kai, ranar Lahadi, 1 ga Oktoba, 2023
‘Yan uwana ‘yan Najeriya,
Ina farin cikin yi muku jawabi a yau, ranar cikar ƙasarmu shekaru 63 da samun ‘yancin kai, a matsayina na shugaban ƙasarmu mai albarka, kuma zallar ɗan uwanku ɗan Nijeriya.
- A wannan rana mai muhimmanci mai cike da fatan alheri, muna jinjina ga iyayenmu da suka kafa Nijeriya, mazansu da matansu. Ba don su ba, da ba a samu ƙasar Nijeriya ba. Gwagwarmayarsu, sadaukarwarsu, da jagorancinsu ne suka haifar da ‘yantacciyar ƙasar Nijeriya mai mulkin kanta.
- A wannan lokacin, muna karfafa wa juna gwiwar cewa a matsayinmu na ‘yan Nijeriya, Allah ya yi mana baiwa a dunƙule da kuma a daidaikunmu. Babu wanda ya fi wani a cikinmu. Nasarorin da Nijeriya ta cimma su ne abin alfaharinmu. Ƙalubalen da muka jure wa su ne ke ƙarfafar mu. Kuma babu wata ƙasa ko wani iko a duniya da zai iya danƙwafe mu daga isa matsayin da ya dace da mu. Wannan ƙasar taku ce, ‘yan uwana. Ku so ta, ku karrama ta a matsayinta ta ƙasarku ta kanku.
- Nijeriya ta isa kasa a bar misali bisa yanayin zubi da tsarinta. Allah ya azurta mu da kabilu, addinai, da al’adu dabam-dabam. Sai dai dankon zumuncin dake tsakaninmu ya na da matuƙar ƙarfi ko da yake ba ganin sa ake ba. Mun haɗu kan buri guda ɗaya na samar da zaman lafiya da cigaban al’umma, da fata guda na bunƙasar arziki da hadin kai, da kuma manufofin haɗaka na juriya da adalci.
- Samar da ƙasa da aka ɗora bisa harsashin aiwatar da waɗannan manufofi masu daraja kan al’ummomi mabanbata ya zamo aiki mai matuƙar albarka da yake fama da ƙalubale. Waɗansu mutanen sun ce bai kamata a samu ‘yantacciyar kasar Nijeriya ba. Wasu sun ce ƙasarmu za ta rushe. Har abada su na bisa kuskure. A nan, ƙasarmu ta kafu kuma a nan za ta tabbata.
- A bana, mun tsallake wani siraɗi mai muhimmanci a tafarkinmu na tabbatar da cigaban Nijeriya. Zaɓen da muka yi wa gwamnatin dimokraɗiyya ta bakwai a jere, na nuna cewa ƙasarmu ta yi riko da tsarin dimokuraɗiyya da aiki da doka.
- Ranar da na kama mulki, na ɗauki alƙawurra kan yadda zan shugabanci wannan babbar ƙasa ta mu. Daga cikin alkawurran har da yi wa tattalin arzikinmu garanmbawul domin samar da tsaro ga rayuka, ‘yanci, da walwalar al’umma.
- Na ce ɗaukar tsauraran matakai ya zama wajibi domin dora ƙasarmu kan tafarkin walwala da bunƙasar tattalin arziki. A ranar na sanar da kawo ƙarshen tallafin man fetur.
- Ina sane da wahalhalun da suka biyo baya. Idanuna suna gani kuma zuciyata ta na ƙunci. Ina son in bayyana muku dalilin da ya sa wajibi mu cigaba da daurewa a cikin wannan mawuyacin hali. Waɗanda ke son a cigaba da tallafin man fetur da mummunan tsarin sauyin kuɗaɗen waje, mutane ne da ke son gina tafka-tafkan gidaje a cikin fadama. Ni ba haka nake ba. Ni ba zan gina mana gida a bisa tubalin toka ba. Idan muna son gidanmu ya yi ƙwari, ya daɗe dole ne mu gina shi kan tsandauri.
- Gyara abu ne mai ciwo, amma shi ne abin da ci gabanmu da ɗaukakarmu ke buƙata. A yanzu muna ɗauke da wahalhalun da za su kai mu zuwa ga makomar da za a raba arzikin ƙasarmu mai yalwa bisa adalci ga kowa da kowa maimakon wasu tsirarun mahandama su tattare a wurinsu. Zamu samar da Nijeriyar da za a mayar da yunwa, fatara, da wahala su zama tsohon labari.
- Ba na farin cikin ganin al’ummar ƙasar nan na fama da wahalar da ya kamata a ce an sauke ta a shekarun da suka wuce. Zan so a ce babu waɗannan wahalhalun a yanzu. Amma dole ne mu daure idan muna son samun makoma ta gari.
- Gwamnatina na yin bakin ƙoƙarinta wurin sassauta wannan wahala. Yanzu zan bayyana muku matakan da muke ɗauka domin rage wannan raɗaɗin da magidanta da iyalai ke fama da su.
- Mun fara ɗaukar matakan sauya tsarin tafiyar da gwamnati domin samar da daidaton tattalin arziki, yaki da hauhawar farashi, bunƙasa ayyukan masana’antu, samar da tsaron rayuka da dukiya, da kuma tallafa wa talakawa da sauran mabukata.
- Bisa tattaunawarmu da ‘yan ƙwadago, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, muna gabatar da karin albashi na farko inda za mu ƙara mafi ƙarancin albashin gwamnatin tarayya ba tare da ƙara hauhawar farashi ba. A tsawon watanni shida masu zuwa, kananan ma’aikatan Gwamnatin Tarayya za su samu ƙarin Naira Dubu Ashirin da Biyar kowanne wata a albashinsu.
- Domin kawo ci gaba a yankunan karkara, mun kafa asusun tallafi kan samar da kayayyakin more rayuwa domin jihohi su bunƙasa bangarorin dake da muhimmanci a yankunansu. Tuni jihohi suka karɓi kuɗi domin ba da tallafin sassauta raɗaɗin hauhawar farashin abinci da sauran buƙatun yau da gobe.
- Bunƙasa tattalin arziki ta hanyar rage farashin sufuri na da matuƙar muhimmanci. Dangane da haka ne muka buɗe wani sabon babi a fannin sufuri ta hanyar samar da motocin haya masu amfani da iskar Gas a faɗin ƙasar nan. Wadannan motoci za su caji kuɗi mai sauƙi da bai kama ƙafar yadda ake biya yanzu ba.
- Ba da jimawa ba kayan aikin sauya motoci masu amfani da fetur zuwa gas za su fara isowa ƙasar nan saboda mun dauki matakan takaita lokacin da aka saba dauka kafin shigo da su. Kuma za mu kafa wurin bada horo a faɗin ƙasa domin koyarwa da bada sababbin damarmaki ga masu harkar sufuri da kuma masu kafa masana’antu. Wannan lokaci ne mai muhimmanci da ƙasarmu ta rungumi hanya mafi inganci wurin samarwa tattalin arzikinmu makamashi. Samar da wannan sauyin, kafa sabon tarihi ne.
- Na ɗauki alƙawarin tsaftace barnar da ta yi wa Babban Bankin Kasa dabaibayi. Wannan aikin an riga an fara. An kafa sabon shugabanci a Babban Bankin. Kuma mai bincike na musamman da na nada na gab da gabatar da rahotonsa kan kurakuran da aka samu a baya da kuma hanyoyin da za a magance afkuwar hakan nan gaba. Daga yanzu, dokokinmu na tasarrufi da kuɗi za su amfani kowa da kowa ne maimakon masu iko da masu kuɗi kaɗai.
- Dokar haraji mai hikima na da muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki da adalci. Na ƙaddamar da kwamitin sauya fasalin tsarin haraji domin inganta tattara haraji a ƙasar nan da kuma magance dokoki marasa adalci ko masu kawo tarnaƙi ga ci gaban kasuwanci da bunƙasar tattalin arziki.
- Domin bunƙasa samar da aikin yi da kuɗin shiga ga mazauna birane, mun samar da asusun zuba jari ga kamfanonin da suka nuna alamar makoma ta gari. Haka kuma mun ƙara zuba jari a kanana da matsakaitan kamfanoni.
- Daga wannan watan, za a kara gidaje miliyan 15 kan waɗanda ake bai wa tallafin kuɗi kai tsaye domin rage masu raɗaɗi.
- Gwamnatina a ko da yaushe za ta ci gaba da bai wa tsaron al’umma muhimmancin gaske. Mun bunƙasa haɗin kai da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro. An ɗora wa manyan hafsoshin sojin muhimmin aikin farfaɗo da karsashin rundunonimu.
- A nan, nake jinjina da yabo ga dakarun tsaronmu, da suke ba mu kariya tare da tabbatar da tsaron ƙasarmu. Da yawansu sun riga mu gidan gaskiya. Muna tuna su a yau tare da iyalansu. Za mu bai wa dakarunmu kayan aikin da za su sauke nauyin da ke kansu a madadin al’ummarmu.
- Zamu ci gaba da nada mutane bisa muhimman muƙamai daidai da tanadin tsarin mulki na yin adalci ga kowa. Za a cigaba da kulawa da mata, matasa da masu buƙatu na musamman a wadannan naɗe-naɗen.
- Zan yi amfani da wannan dama domin taya Majalisun Dokoki na Ƙasa murna kan rawar da suka taka wurin kafuwar wannan gwamnati ba tare da bata lokaci ba ta hanyar gudanar da ayyukan da tsarin mulki ya ɗora musu na tantance wadanda za a nada da kuma sa ido kan yadda suke gudanar da ayyukansu.
- Haka kuma ina taya ɓangaren Shari’a murna a matsayinsu na ginshikin dimokraɗiyya da adalci.
- Ina kuma taya murna ga ƙungiyoyinmu na ci gaban al’umma da ƙungiyoyin ƙwadago bisa sadaukarwarsu ga dimokraɗiyyar Najeriya. Ba ko da yaushe ra’ayinmu kan zama ɗaya ba amma ina mutunta shawarwarinku. Ku ‘yan uwana ne kuma ina girmama ku.
- ‘Yan uwana ‘yan Nijeriya, tsoro ko kiyayya ba za su kawo mana ci gaba ba. Za mu iya samun ingatacciyar Nijeriya ne kadai ta hanyar ƙwarin gwiwa, tausayi da kuma sadaukar da kai a matsayin dunƙulalliyar ƙasa guda.
- Na yi alƙawari zan ci gaba da mayar da hankali tare da bauta muku cikin amana. Ina kuma gayyatar kowa ya bada gudunmawa wurin ci gaban ƙasarmu abar kaunarmu. Za mu iya. Ba makawa za mu yi. Kuma tabbas za mu yi nasara!!!
- Baki ɗayanku ina taya ku murnar cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai.
- Nagode da sauraro.
- Allah ya albarkaci Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya.
