An kashe ɗalibin jami’a saboda budurwa a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wasu da ake zargin ɗalibai ne sun kashe abokin karatunsu, Abubakar Nasir Barda, a jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutsinma ta jihar Katsina.

Ɗalibin ya gamu da ajalinsa a hannun ‘yan uwansa ɗalibai bayan da suka lakaɗa masa duka, a dalilin yi wa wata ɗaliba mace magana a jami’ar wadda ake kyautata zaton budurwar ɗaya daga cikin ɗaliban da suka yi aika aikar ne.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, ASP Sadiq Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.

Jami’in ya bayyana cewar, an kama mutane 6 daga cikin 8 da ake zargi da aikata kisan ɗalibin wanda ke aji biyu a jami’ar ta FUDMA.

Rundunar ta tabbatar da cewa hamayya ce a kan wata budurwa tsakanin marigayin da sauran ɗalibai ya haddasa lamarin.

“Lamarin ya afku ne sakamakon rashin fahimta tsakanin ɗaliban dake hamayya a kan wata yar uwarsu ɗaliba mace, ta yadda har lamarin ya jawo mumman abin ban tausai da ya kai ga rayuwar wani daga cikin ɗaliban ta salwanta.

“Rundunar yan sanda ta ɗauki lamarin da muhimmanci sosai, kuma yanzun haka tana cikin gudanar da bincike don gudanar da ainihin cikakken bincike game da abinda ya faru, kuma yanzun haka mun yi nasarar kama ɗalibai 6 cikin 8 dake da alaƙa da lamarin.” Inji Sanarwar

Haka zalika, mahaifin ɗalibin Ibrahim Barda, ya nuna matuƙar takaicinsa kan kisan ɗan nasa.

Ya zargi hukumar jami’ar da sakaci kan lamarin wanda hakan ya kai ga rasa rayuwar ɗan sa.

Daga ƙarshe, ya yi kira ga hukumar makarantar da ta tabbatar ta ɗauki matakin qwato wa marigayin haƙƙinsa don kare faruwar hakan nan gaba.

By Editor