Ranar Samun ‘Yancin Kan Ƙasa: Tinubu ya yi wa ma’aikata ƙarin albashi na wucin-gadi

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana ƙarin albashi ga ma’aikatan gwamnati don rage musu raɗaɗin cire tallafin mai.

Ya sanar da hakan ne a jawabinsa da ya yi wa ‘yan ƙasa da safiyar Lahadi albarkacin Ranar Samun ‘Yancin Kan Ƙasa, 1 ga Oktoba, 2023.

Game da ƙarin, Tinubu ya ce ƙaramin ma’aikaci zai samu ƙarin N25,000 a albashinsa har na tsawon wata shida.

Wannan na nufin ma’aikacin gwamnatin tarayya da ke karɓar albashi N30,000, yanzu N55,000 zai riƙa karɓa har na tsawon wata shida.

Da alama dai ƙarin albashin na wucin gadi ne, kuma Shugaban bai yi ƙarin haske kan lokacin da ƙarin zai fara aiki ba.