Cutar Mashaƙo: Kano ta samu tallafin alluran rigakafi miliyan huɗu daga UNICEF

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya ba wa Kano da sauran jihohi alluran riga-kafin cutar Mashaƙo wadda aka fi sani da Diphtheria guda miliyan 9.3.

Daga cikin adadin da hukumar ta ba wa jihohin da aka samu vullar, UNICEF ta tura wa Jihar Kano alluran riga-kafin guda miliyan huɗu, a matsayin Kano na jihar da cutar ta fi ƙamari.

Wakilin UNICEF, Dokta Rownak Khan, Sauran jihohin da za su amfana da tallafin alluran riga-kafin na UNICEF su ne Bauchi, Borno, Yobe, Katsina, Kaduna da kuma Jigawa.

Hukumar ta ƙara da cewa nan da makonni masu zuwa za ta samu ƙarin alluran rigakafin guda miliyan huɗu ga gwamnati domin taimaka mata wajen yaƙar cutar.

Kawo yanzu cutar Diphtheria ta hallaka mutum 453 a Nijeriya kuma yawancinsu ƙananan yara ne ’yan shekaru huɗu zuwa 15, waɗanda ba a taɓa yi musu allurar rigakafin ba.

Mutum sama da 7,000 ne aka tabbatar suna ɗauke da cutar da cikin mutane sama da 11,500 da ake zargin su da alamunta.

UNICEF ta ce yara sama da miliyan biyu ne a Nijeriya ba a taɓa yi wa allurar rigakafin cutar ba, don haka ta jaddada buƙatar ɗaukar duk matakan da suka dace na magance ta.

By Editor