Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da hatsarin jirgin sojoji ya rusa da mutum 32 a Ondo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci-gaban Sararin Samaniyar Nijeriya, Festus Keyamo (SAN), ya tabbatar da labarin hatsarin wani jirgin sojoji da ke ɗauke da mutane 32 a yankin Igbokoda na Jihar Ondo a Kudu maso Yammacin Nijeriya.

Rahotanni sun nuna cewa, jirgin, mai lamba 931, yana tafiya ne daga Benin zuwa Legas a lokacin da aka neme shi aka rasa da misalin ƙarfe 9:13 na safiyar yau Litinin, lamarin da ya sanya jami’an kula da zirga-zirgar jirage shiga gudanar da bincike.

Keyamo a wata sanarwa, ya ce yunƙuri da dama na ji ta bakin matuƙa da jami’an jirgin daga masu kula da zirga-zirgar bai yi nasara ba, lamarin da ya sanya hukumomi ƙaddamar da atisayen nemo sa. Ya ce, bayanan da suka samu daga bisani sun tabbatar da cewa jirgin ya yi hatsari ne a kusa da wani sanansanin Sojin Sama da ke garin Igbokoda, inda aka kuma gano buraguzan sassan jirgin.

A cewar ministan, ana gudanar da bincike da ƙoƙarin ceto mutanen da iftila’in ya shafa yayin da hukumomi suke aiki domin fitar da ainihin yadda al’amarin ya kasance. Wani bayani da aka samu ya nuna cewa fasinjoji guda 25 ne jirgin yake ɗauke da su da jami’an jirgi su bakwai, inji ministan.

Saidai ministan ya bayyana cewa kula da gudanarwar jirgin sojojin ba ya ƙarƙashin ikon ma’aikatarsu da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama na Fararen Hula ta Ƙasa (NCAA), amma ya tattauna da Shugaban Rundunar Sojin Saman Nijeriya, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke kan al’amarin, yana mai tabbatar masa da samun cikakken haɗin kan ma’aikatar akan aikin bincike da ceton da ake gudanarwa.

By Babaji

Leave a Reply