Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta tasa ƙeyar Malami da ɗansa zuwa kurkukun Kuje

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja, ta umarci a tsare Abubakar Malami, wato tsohon Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a a gidan yarin Kuje har zuwa lokacin da za ta sake sauraron ƙarar da aka shigar akansa da neman bada belinsa.

Alƙali Emeka Nwite yayin hukuncin, ya kuma umarci a tsare ɗan Malami, Abdulaziz da, kuma matarsa Bashir Asabe har zuwa lokacin da za a bada belinsu.

An gurfanar da mutane ukun ne bisa zargin su da hannu a laifuka guda 16 masu alaƙa da badaƙalar kuɗaɗe a yau Talata.

Baki ɗayansu sun musanta zarge-zargen da ake musu wanda Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta shigar akansu a ƙarƙashin jagoran Lauya Ekele Iheanacho.

To saidai a ɗaya ɓangaren kuma, Lauyan waɗanda aka shigar ƙara, wato Joseph Daudu ya ce ya miƙa takardar buƙatar bada belinsu tun gabanin gurfanarwar, wadda Iheanacho ya ce a jiya da misalin ƙarfe 3 na rana aka yi haka, don haka sai an bada ranar bada amsa daga jagorancin kotun.

Mai Shari’a Nwite ya bayyana cewa, sai an kammala aiki akan ƙararrakin da aka gabatar wa kotun kafin bada amsa akan takardun.

Daga nan ne alƙalin ya umarci a tsare su a kurkukun na Kuje har zuwa ranar 2 ga watan Junairu domin sauraron ƙarar neman belin.

By Babaji