MOPPAN ta jinjina wa Kabir Jammaje bisa samar wa mambobinta fagen karatu kyauta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta ƙasa (MOPPAN) da ɗaukacin ƴan masana’antar Kannywood, sun yaba wa Malam Kabir Musa Jammaje bisa samar da shirin bada ilimin kararun darasin Turanci a kyauta ga mambobinsu.

MOPPAN ta ce, ƙoƙarinsa na inganta jaruman harkar fim, daraktoci, jami’an shirya fim da sauransu a masana’antar, abu ne da zai taimaka wajen bunƙasa harkokinsu.

A wata takarda da Kakakin ƙungiyar, Ibrahim Amarawa ya fitar, MOPPAN ta bayyana cewa a wannan zamani na ci-gaba, ƙwarewa a yaren Turanci ba iya nagarta ba ce, abu ne da zai buɗe ƙofar wasu damarmakin wajen tara masoya da haɗin-gwiwa mai ƙarfi tsakanin ma’abota ƙirƙira.

Ta ƙara da cewa, ƙoƙarin Jammaje wajen inganta lamuran Kannywood da ƴaƴanta ya nuna yadda ya sadaukar da matsayinsa ga ci-gaban masana’antar.

A cewarta hakan ba iya koyar da yaren na ya tsaya ba, saidai zuba jari ne ga goben mutane da dama waɗanda su ne ginshiƙin sinimar Hausa.

Don haka ta aike masa da saƙon godiya na musamman ginin yadda yake fatan wasu su yi nasara a rayuwa, lamarin da ta ce zai kawo gagarumar ci-gaba a gare su da ma masana’antar baki ɗaya, tana mai masa fatan nasara a harkokin rayuwarsa.

By Babaji