
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar PDP ta shigar ta ƙalubalantar hukuncin da ya hana Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) amincewa da sakamakon babban taron jam’iyyar da aka gudanar a Ibadan na Jihar Oyo a 2025.
Tun da farko, Babbar Kotun Tarayya ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a James Omotosho ta yanke hukunci a ranar 31 ga Oktoba inda ta hana INEC amincewa da sakamakon taron PDP na ƙasa da aka gudanar a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba a Ibadan.
Sai dai jam’iyyar PDP ta ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin, amma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke hukunci baki ɗaya ta hanyar kwamitin alkalai uku, inda ta bayyana cewa Hujjojin da PDP ta gabatar ba su da inganci.
Kotun ta kuma bayyana ƙarar a matsayin mara tushe, tare da umartar jam’iyyar PDP ta biya tarar naira miliyan biyu (N2,000,000) a matsayin kuɗin shari’a.
Kotun ta tabbatar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na dakatar da babban taron jam’iyyar na ƙasa, tare da yin watsi da ƙarar ɗaukaka kara da tsagin jam’iyyar da Taminu Turaki ke jagoranta ya shigar domin a soke hukuncin.
Alkalan kotun sun bayyana cewa babu wani kuskure a hukuncin da kotun ƙasa ta yanke na hana gudanar da taron, don haka suka tabbatar da cewa dakatarwar na nan daram.
Haka kuma kotun ta kori dukkan hujjojin da masu ɗaukaka ƙara suka gabatar, tana mai cewa ba su da cikakken tushe na shari’a.
Baya ga hakan, kotun ta umarci tsagin Turaki da su biya tarar Naira miliyan 2 a matsayin kuɗin shari’a ga ɓangaren da suka yi nasara.
A wani bangare na hukuncin kuma, kotun ta bayyana cewa taron da bangaren Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed suka gudanar bai da inganci, inda kotun ta siffanta shi a matsayin taro mara ingancin doka.
Sai dai kuma a gefe guda, kotun ta jaddada korar wasu daga cikin magoya bayan Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, matakin da bangaren Kabiru Turaki suka dauka tun da farko.
Sabon hukuncin na nuni da cewa bangarorin biyu sun samu nasara a wasu bangarori na shari’ar, lamarin da ya kara rikitar da rikicin cikin gida na jam’iyyar.
Rahotanni na nuni da cewa ɓangarorin biyu na shirin garzayawa zuwa Kotun Koli domin neman hukunci na ƙarshe kan rikicin da ke addabar jam’iyyar na tsawon lokaci.
