Boko Haram sun sake kashe wani kwamandan soji a Borno

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

‘Yan ta’addar Boko Haram sun kai wani sabon hari kan sansanin sojoji a Jihar Borno, inda suka kashe kwamandan sansanin da wasu sojoji. Harin ya faru ne a ƙaramar hukumar Kukawa da sanyin safiyar ranar Litinin.

Wata majiya daga garin ta bayyana cewa maharan sun kai harin ne kusan ƙarfe 12:30 na dare, inda suka shigo daga ɓangarori daban-daban suka afkawa sansanin sojojin. Wata majiya ta tsaro ta ce maharan sun tilasta wa sojojin janyewa daga sansanin, sannan suka kona wasu motocin sojoji tare da kwashe makamai da alburusai.

A watan da ya gabata dai maharan sun kai hari kan sansanin amma sojoji sun daƙile su tare da kashe wasu daga cikinsu. Sai dai a wannan karon an ce sansanin ya faɗi hannun maharan, lamarin da ɗan majalisar da ke wakiltar Kukawa Local Government Area ,Karta Maina Ma’aji Lawan, ya bayyana a matsayin abin takaici. Wannan hari na zuwa ne bayan wani hari da aka kai a garin Ngoshe, inda aka kashe wasu sojoji da fararen hula.

By ukarofi