Gwamnan Zamfara ya bar PDP zuwa APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya yi murabus a hukumance daga jam’iyyar PDP tare da bayyana koma wa mai mulki (APC) sa’o’i kaɗan da bayyana sha’awarsa ta sauya sheƙa.

A yau Litinin ne mai taimaka masa akan harkokin labarai, Nuhu Anka ya tabbatar da rahoton ga manema labarai a wata sanarwa, inda ya ce gwamnan ya ɗauki matakin ne bayan nazarin mai zurfi da shawarwari daga masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar jihar.

A cewar sanarwar da Nuhu Anka ya fitar, Gwamna ya bar PDP ne bisa dagulewar al’amura da ke cikin jam’iyyar da kuma tabbatar ɗorewa da ci-gaba a jiharsa.

Ya bayyana cewa, hakan na zuwa ne sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye PDP, wanda aka gagara magancewa a matakin jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

A cewarsa, rashin daidaita al’amuran jagorancin PDP ya haddasa rashin tabbas game da makomar ‘yan siyasa da dama da koma-baya ga harkokin shugabanci.

Gwamna Lawal ya kuma bayyana godiyarsa ga jam’iyyar da mambobinta bisa haɗin kai da ya samu da tallafi a harkokin siyasarsa.

By Babaji