
Daga BELLO A. BABAJI
Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da tsige wasu kwamishinonin zaɓe guda uku bisa laifin bijirewa dokokin kundin dokar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC.
Tun a shekarar 2023 ne aka dakatar da manyan jami’an zaɓen, biyo bayan neman buƙatar soke naɗinsu da Shugaba Bola Tinubu ya yi, inda ya nemi majalisar da ta tabbatar da hakan.
Kwamishinonin sune na jihohin Adamawa, Sokoto da Abia.
Cikakken bayani zai zo daga baya….
