Daga UMAR GARBA a Katsina
Ƙungiyar dattawan Jihar Katsina ta buƙaci gwamnatin tarayya akan ta gaggauta sakin farfesa Usman Yusuf, tsohon babban sakataren hukumar inshorar lafiya ta ƙasa (NHIS) ba tare da wani sharaɗi ba.
A cewar sakataren ƙungiyar Aliyu Sani Muhammad, an dawo da farfesa Usman Najeriya daga ƙasar Amurka inda yake aiki a matsayin ƙwararren likitan dashen ƙashi domin ya jagoranci hukumar NHIS, saboda haka bai kamata a kama shi a tsare ba ba tare da wasu ƙwararan hujjoji ba.
Saboda haka ƙungiyar na ganin an tsare babban likitan ne saboda sukar gwamnati da yake yi a cikin hirarraki da yake a kafafen yaɗa labarai.
Rahotanni daban daban sun ruwaito yadda hukumar EFCC ta kai samame gidansa da ke Abuja a makon da ya gabata, inda ta kama shi a gaban iyalansa.
Daga baya an gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zarginsa da laifin zamba inda daga baya kuma kotu ta tura shi gidan yari.
Saboda haka ne ƙungiyar dattawan ta Katsina ta bayyana cewa Yusuf bai yi wani laifi ba, kuma ana tsare da shi ne saboda ya faɗi albarkacin bakinsa da tsarin mulkin ƙasa ya ba shi.
Sakataren ƙungiyar Aliyu Sani Muhammad, ya yiwa gwamnatin shugaba Bola Tinubu tambayoyi, inda ya tambayi shugaban ƙasar “ko ana tauye ‘yancin dimukraɗiya ne?”.
Daga nan sai sakataren ƙungiyar ya yi watsi da tuhumar da ake yi wa Yusuf cewa, ya baiwa ɗan uwansa kwangila a cewar sakataren wannan tuhumar abun dariya ne, ya cigaba da cewa kwangilar ƙarama ce idan aka kwatanta da kwangilar aikin hanyar Lagos-Calabar wadda aka ce an baiwa ɗan shugaban ƙasar Seyi Tinubu kan Naira tiriliyan 16, inda ya bayyana cewa kwangilar ta saɓa wa doka.
“Har yanzu Amurkawa na buƙatarsa, kuma duk faɗin duniya ana buƙatarsa, ba mu da irinsa a Najeriya”. Inji sakataren.
A nasa ɓangaren, Sanata Mamman Abubakar Ɗanmusa, muƙaddashin shugaban ƙungiyar, ya gargaɗi shugaba Tinubu kan sakamakon ci gaba da tsare Farfesa Yusuf, inda ya ce hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
