
Daga BELLO A. BABAJI
An zaɓi Agbo Major a matsayin sabon shugaban jam’iyyar NNPP a yayin taron jam’iyyar na ƙasa a Otal ɗin RockView dake Apapa a jihar Legas.
Taron ya samu halartar daliget da dama da mambobin jam’iyyar daga sassan Nijeriya.
Sauran waɗanda aka zaɓa sun haɗa da; Oginni Olaposi a matsayin sakatare na ƙasa; Felix Chukwurah a matsayin mataimakin shugaban jam’iyya (na Kudu); Adetoyese Omokanye a matsayin ma’aji; mataimakin shugaban jam’iyya na Arewa, Bayo Muhammed da Abdulrasaq Abdulsallam a matsayin sakataren yaɗa labarai.
Sai Aisha Kade a matsayin jagorar mata (woman leader), Edward Ofomona a matsayin shugaban matasa da kuma Omolara Johnson a matsayin sakatariyar shirye-shirye.
An gudanar da zaɓen ne a ƙarƙashin jagorancin kwamitin Amintattun jami’iyyar (BoT) da kuma Kwamitin Ayyuka (NWC) bisa umarnin hukuncin Kotun Tarayya dake Abia na ranar 1 ga watan Nuwamban 2024.
Kotun ta kuma umarci Hukumar Zaɓe (INEC) da ta tantance tare da tabbatar da sababbin jagororin jam’iyyar.
