
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Jihar Kogi ta shigar da takardar ɗaukaka ƙara a Kotun Ɗaukaka ƙara dake Abuja bisa hukuncin Babbar Kotun Tarayya na tsige Ohinoyi na Masarautar Ibira, Tijani Ahmed Anaje.
A ranar Talata ne Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a na jihar, Muzi Abdullahi, wanda shi ne na biyu cikin masu ɗaukaka ƙarar, ya bayyana hakan a Lokoja.
Ya ƙalubalanci hukuncin ƙarar da Daudu Adeku-Ojiah, Hussaini Yusuf da Abdulrahmaam Suberu suka shigar wanda ke ƙalubalantar naɗin Ahmed Anaje da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello ya yi.
Mutane ukun da shigar da ƙarar sun nemi kotun da ta ayyana naɗin Sarki Anaje a matsayin haramtacce kasancewar ba a bi hanyoyin da dokar naɗa Ohinoyi na Masarautar ta tsara ba.
Gwamna Ododo da Antoni-Janar Muzi Abdullahi ne waɗanda suka ɗaukaka ƙarar don rushe hukuncin Babbar Kotun inda suka nemi a yi watsi da ƙarar mutane ukun saboda rashin nagarta, don tabbatar da Anaje a matsayin halasttaccen sarkin.
