NAHCON ta ƙara wa’adin rajista ga mahajjatan 2025

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta sanar da ƙara wa’adin yin rajista ga mahajjatan shekarar 2025.

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya bayyana hakan a ranar Talata, ta ofishin Kodinetan tawagar yaɗa labaran hajji na Ƙasa, Ibrahim Abubakar Nagarta.

Shugaban hukumar ya ce an ƙara kwanaki 10 na yin rajistar ne domin bai wa wasu maniyyata damar shiga sahun masu zuwa aikin hajji a wannan shekarar.

Hakan na zuwa ne kwana biyu da wa’adin rajistar ya ƙare, a ranar 2 ga watan Fabrairu.

Farfesan ya kuma yi kira ga maniyyatan da su yi amfani da damar hakan wajen yin rajistar, ya na mai cewa babu ƙarin wani lokaci kuma daga wannan.

By Babaji