DA ƊUMI-ƊUMi: Majalisar Dattawa ta tantance Omokri da Fani-Kayode a matsayin jakadu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kwamitin Majalisar Dattawa akan al’amuran ƙasashen waje ya tantance Reno Omokri a matsayin jakada bayan miƙa sunansa da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa majalisar.

A yau Alhamis aka tantance Omokri, wanda tsohon mataimaki ne na musamman ga shugaban ƙasa.

Idan za a iya tunawa, sanya Omokri a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda za a naɗa jakadu a gwamnatin Shugaba Tinubu ya janyo cece-kuce acikin sanatoci da wasu ƴan Nijeriya bisa zargin sa da kiran Shugaba Tinubu da “dillalin ƙwaya”.

Amma duk da haka a yau ya je gaban majalisar bisa umarnin Tinubu na a tantance shi a matsayin jakada kuma aka yi hakan.

Haka kuma, kwamitin ya tantance tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode bayan ya halarci zaman majalisar. Tuni aka ba Kayode, wanda kuma tsohon Ministan Al’adu ne damar kama aiki shi ma a matsayin jakada.

Kazalika, Abdulrahman Dambazau, wato tsohon Ministan Harkokin Cikin gida, wanda shi ma an tantance shi a irin matsayin.

A cewar jagoran sanatoci, Sanata Bamidele Opeyemi, an yi amfani da tsarin ‘duƙa ka tafi’, wato “bow and go” a matsayin ɓangare na tantancewar duba da cewa yana daga cikin tsarin majalisar.

Sannan duk wanda ya taɓa zama ɗan majalisar dokoki ta ƙasa, ya riga ya samu wannan damar kai-tsaye.

By Babaji