DA ƊUMI-ƊUMI: Rahoto ya nuna Maitaimakin Gwamnan Bayelsa ya rasu sa’o’i bayan ya yanki jiki ya faɗi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo ya rasu a yau Alhamis.

Da misalin ƙarfe 1:30 na rana aka ruwaito cewa ya yanki jiki ya faɗi a ofishinsa, inda aka gaggauta garzayawa da shi zuwa Babban Asibitin Tarayya da ke Birnin Yenagoa, sannan aka tabbatar da rasuwarsa jim-kaɗan bayan haka.

A ranar 5 ga watan Satumban shekarar 1965 aka haifi marigayin, kamar yadda majiyoyi suka shaida.

Majiyoyi daga gidan gwamnatin jihar sun bayyana shi a matsayin mai ƙoƙarin kiyaye aikinsa bisa sadaukarwa da jajircewa.

A cewar ShaharaReporters, Mataimakin gwamnan ya shiga mawuyacin hali ne a lokacin da aka kai shi sashen gaggawa na asibitin.

Wani ɗan gidansu da ya gana da manema labarai ya tabbatar mutuwar jim-kaɗan da kai shi asibitin.

By Babaji