Gwamnatin Katsina ta amince ta ba malaman makarantun ƙauyuka alawus na Naira 30,000

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Haka kuma gwamnatin jihar na shiri na musamman don horas da malamai tare da kafa cibiyoyin horo a yankunan Katsina, Daura da Funtua domin inganta dabarun koyarwa da ingancin ilimi a jihar.

Gwamnatin ta amince da haka ne a zaman majalisar zartarwa ta Katsina a karo na 18 inda ta kuma amince da wasu mahimman ayyuka a jihar.

Haka kuma ta amince da kafa kwamitin kula da makarantun koyon kiwon lafiya masu zaman kansu don inganta koyar da kiwon lafiya a faɗin jihar.

Majalisar zartarwa ta kuma amince da gina gidaje guda 150 da samar da fulotai 350 a garin Katsina.

Gwamnatin za ta fara aiwatar da sabunta tsare-tsaren birane na Katsina, Daura da Funtua domin cigaban tsarin sabunta birane.

Ta wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar kuwa majalisar zartarwa ƙarƙashin gwamna Dikko Raɗɗa ta amince da gina cibiyar sarrafa rogo a Batsari domin inganta noman rogo da haɓaka tattalin arzikin jihar.

Duk a zaman, majalisar zartarwa ta amince da shirin sauƙaƙa kasuwanci na shekarar 2026 domin jawo hannun jari da kuma taimaka wa jihar samun kuɗaɗen shiga.

Za ta samar da kayan aiki a cibiyar koyon sana’o’i Na garin Katsina (Katsina (Craft Village) tare da samar da ruwan sha a garin Tsagero a ƙaramar hukumar Rimi ƙarƙashin shirin Small Town Water Scheme.

By ukarofi