
Daga BELLO A. BABAJI
An tabbatar da mutuwar Misis Patience Martha Umo Eno, matar Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Fasto Umo Eno.
Kwamishinan Labarai na jihar, Ini Ememebong ya faɗi hakan cikin Wata sanarwa da ya fitar da asubahin ranar Juma’a.
Ya ce, matar da rasu ne a wani asibiti a daren ranar Alhamis a yayin da iyalanta ke kusa da ita.
Ememebong ya ƙara da cewa, iyalan marigayiyar sun miƙa al’amarin ga Ubangiji tare da roƙon addu’a daga wajen al’umma da taimakon su a lokacin ƙuncin da suka tsinci kansu.
Gwamna Eno ya yi godiya ga waɗanda suka tsaya a kan halin iyalin nasa tare da tabbatar wa al’umma cewa zai ɗora daga inda ya tsaya a ƙoƙarin da ya ke yi na ayyuka a jihar.
