Eguavoen zai cigaba da jagorancin Super Eagles yayin da Madugu ya zama kocin Super Falcons

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kwamitin Zartarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF), ya tabbatar da zaɓin kwamitin gudanarwa da ci-gaba na a bai wa Daraktan gudanarwa, Augustine Eguavoen damar cigaba da zama kocin ƴan Super Eagles.

Eguavoen, mai shekaru 58 ya jagoranci tawagar a wasanni uku da suka buga a baya da ƙasashen Jamhuriyar Benin da ta doke da ci 3 da 1 da kuma Ruwanda a wasanni biyu.

Hakan ya nuna cewa, kocin shi zai jagoranci Super Eagles a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka na 2025 da za a yi a wata mai zuwa da Libya.

Haka nan kwamitin ya tabbatar da koci Justin Madugu a matsayin wanda zai jagoranci ƴan ɓangaren mata, wato Super Falcons zuwa lokacin da za a naɗa wani koci.

Gasa ta gaba da ƙungiyar za ta fafata a ciki ita ce ta kofin ƙasashen Afirka na 2025 da za a yi a Morocco.

By Babaji