
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar Hisbah a Jihar Katsina ta bayyana jin-daɗinta tare da godiya ga Majalisar Dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Nasiru Yahaya bisa amincewa da suka yi na kafa hukumar.
Shugaban hukumar, Dakta Aminu Usman wanda aka sani da Abu Amar ya bayyana hakan a lokacin da tawagarsa suka kai ziyarar girmamawa ga kakakin.
Dakta Usman ya faɗi wasu nasarori da hukumar ta samu tun daga kafuwar ta inda ta fara da ziyarar ɓangarori daban-daban na malaman addinin Musulunci domin neman haɗin-kai .
Ya ƙara da cewa, hukumar ta kuma ziyarci hukumomin tsaro tare da sarakunan Katsina da Daura domin samun haɗin-kai wajen dawo da ɗa’a acikin al’umma musamman matasa a faɗin jihar.
Abu Amar ya kuma faɗi wasu nasarori da hukumar ta samu da suka haɗa da; sasanta zaman auratayya fiye da 1000 da daƙile sana’ar ‘DJ’ wacce ke lalata tarbiyyar matasa.
“Haka kuma, mun sasanta rigingimun basussuka dom haka mutane ke zuwa wajen hukumar fiye da kotu.”
Ya kuma yi kira ga majalisar da ta sake duba dokar da ta kafa hukumar don akwai wasu ƙalubalen da hukumar ke fuskanta wajen gudanar da ayyukanta.
A jawabinsa, Kakakin Majalisar ya yaba da irin yadda hukumar ke tafiyar da ayyukanta inda ya yi kira gare ta da ta kasance mai aiki don Allah a dukkan al’amuran su.
Game da buƙatar hukumar na kwaskwarima ga dokar da ta kafa hukumar kuwa, kakakin ya ce, doka na buƙatar gyare-gyare a lokaci-bayan-lokaci don hakan za su zauna da jami’an hukumar domin a tattauna muhimman abubuwa.
