Daga ƙarshe Gwamnan Akwa-Ibom ya koma APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Umo Eno ya koma Jam’iyyar APC daga babbar jam’iyyar adawa (PDP).

Ya bayyana hakan ne a gidan gwamnatin jihar dake Uyo, ranar Juma’a.

Gwamnan ya ce, hakan ya biyo bayan shawarwari ne da jiga-jigan masu-ruwa-da-tsaki na tsawon watanni uku.

Ya kuma yi godiya ga PDP bisa goyon bayan da ta ba shi a yayin mulkinsa, yana mai cewa lokaci ya yi da ya kamata ya sauya sheƙa domin ci-gaban siyasarsa.

Haka kuma, Eno ya ce hakan da ya yi wani mataki ne na neman ƙara kusanci ga Shugaba Bola Tinubu domin jiharsa ta cigaba da samun riba daga Gwamnatin Tarayya.

Kazalika, ya tabbatar wa al’ummar Akwa-Ibom cewa zai cigaba da yi musu aiki tuƙuru ba tare da la’akari da banbance-banbancen jam’iyya ba.

By Babaji