Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babban hafsan sojin ruwa na Nijeriya ya ce dakarunsa sun yi kaɗan wajen tabbatar da tsaron gaɓar ruwan ƙasar da kuma daƙile satar man fetur.
Da yake magana ta kafar talabijin ta Channels Tɓ a yau Litinin, ɓice Admiral Emmanuel Ogalla ya ce jimillar dakarun rundunar tasa ba su 30,000 da ɗoriya ba.
Sai dai ya ƙara da cewa mahukunta sun ƙara yawan adadin mutanen da suke ɗauka duk shekara domin cike giɓin.
“Za ku sha mamaki idan kuka ji cewa dakarun rundunar sojin ruwa ba su wuce 30,000 da ɗoriya ba,” inji shi.
“Amma kuma muna da gaɓar ruwa mai girman kashi ɗaya cikin uku na faɗin ƙasar Nijeriya baki ɗaya. Muhimmin abu dai shi ne muna ƙoƙarin ƙara yawan dakarun.”
