
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani atisayen leƙen asiri da haɗakar jami’an Rundunar Sojojin Nijeriya, Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) da na Western Nigeria Security Network da aka sani da Amotekun, ya yi sanadiyyar halaka wani babban kwamandan kungiyar ISWAP mai suna Abdussamad Ohida, wanda aka ƙaddamar a Dajin Owo da ke Jihar Ondo.
Rahotanni sun nuna cewa, Ohida, wanda aka sani da Anwar da ke shirin ƙaddamar da wasu munanan hare-haren ta’addanci a wasu jihohin kudancin Nijeriya, an halaka shi ne tare da wasu gungun ‘yan ƙungiyar ta’addancin bayan jami’an tsaron sun kai farmaki a maɓoyarsu a ƙarshen makon da ya gabata.
A cewar majiyoyi, marigayin jagoran ‘yan ta’addar gabanin rasuwarsa shi ne mataimakin jagoran ISWAP a Nijeriya ta Tsakiya, Abu Ikrimah, wanda aka sani da Abu Uwais da aka kama a shekarar 2023. Bayan kama Ikrimah, majiyoyin sun ce Ohida ne ya maye gurbinsa a shugabancin harkokin ISWAP a sassan Arewa ta Tsakiya da kudancin ƙasar, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen shiryawa da aiwatar da ayyukan ‘yan ta’adda.
Majiyoyin sun kuma ce, bayanan da DSS ta samu ta bakin Abu Uwais sun nuna cewa Ohida yana shirin ƙaddamar da kai farmaki akan fararen hula yayin babban zaɓen da ke tafe a 2027 da kuma haddasa tashin-tashina a wasu wurare. An samu wannan bayani ne da haɗin-gwiwar jami’an leƙen asirin Birtaniya, waɗanda kuma da sanya hannunsu ne aka aiwatar da atisayen halaka babban ɗan ta’addan.
Kazalika, wata majiya ta ce Ohida shi ne wanda ya shirya tare da aiwatar da harin Babban Ofishin ‘Yan sanda na Ipele da ke Owo a Jihar Ondo, inda aka yi awon-gaba da bindigu ƙirar AK-47 guda takwas da kuma tarwatsa ofishin da wani abin fashewa.
Ta kuma zayyano harin da aka kai wa shingen binciken sojoji a yankin titin Suleja zuwa Zuba a ranar 28 ga Yuli, 2022, inda aka halaka sojoji, jami’ai da fararen hula da dama. Sannan, ta ɗora wa Ohida laifi a harin gidan yarin Kuje na ranar 11 ga Yuli, 2022; harin Ofishin ‘Yan sanda na Ogaminana a Ƙaramar Hukumar Adavi ta Jihar Kogi da ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan sanda biyar na ranar 23 ga Afrilun 2022 da kuma harin Ofishin ‘Yan sanda na Okene a jihar a ranar 7 ga Fabarairun 2022.
Har ila yau, majiyar ta bayyana cewa, halaka Ohida gagarumar nasara ce wajen ɗaiɗaita jagorancin ISWAP, harkokinsu da kuma ƙoƙarin faɗaɗa ayyukansu a sassan Tsakiya da Kudancin Nijeriya. Wannan na zuwa ne bayan watanni kaɗan da halaka Abu Bilal al-Minuki, wato jagoran ISIS, wanda ke nuna ƙoƙarin dakarun tsaro wajen daƙile ayyukan ta’addanci da masu hannu a ciki a Nijeriya.

