
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Filato ta tabbatar da cewa mutum bakwai sun jikkata a sakamakon wani harbe-harbe da aka ƙaddamar a yankin babban titin Ɓukuru da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu.
Rahotanni sun ce wannan al’amari ya rutsa da wasu ƙananan ‘yan kasuwa da ke koma wa gidajensu daga kasuwa, inda aka yi zargin wasu ‘yan bindiga ne suka buɗe wa motarsu wuta a garin Ɓukuru da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu.
A wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, rundunar ta yi tir da wannan hari, inda ta ce al’amarin ya nufi ‘yan kasuwa ne da suke koma wa gidajensu daga Kasuwar Kara a Ɓukuru. A cewarta, ta samu rahoton harbe-harbe a yankin da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Lahadi, 4 ga Oktoba, 2026, wanda ya yi sanadiyyar raunata mutane bakwai.
Ta kuma ce, a halin yanzu mutanen suna karɓar magani a asibiti, tana mai musu fatan samun waraka cikin ƙanƙanin lokaci.
Akan haka ne Kwamishinan ‘yan sandan, Ayodeji Faniyan ya umarci Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda na reshen bincike da ya gudanar da cikakken bincike kan al’amarin. Ya kuma yi umarci tawagar binciken da ta tabbatar da kamo dukkan masu hannun a ciki tare da gurfanar da su domin su fuskanci hukuncin doka.
Kazalika, rundunar ta shawarci al’umma da su cigaba da zuwa wajen halastattun harkokinsu tare da zama masu lura, tana mai kira a gare su da su ruwaito mata dukkan wani abin zargi ta waɗannan lambobi: 07059473022 da 08038907662.
Haka kuma, ta buƙaci su riƙa ruwaito mata dukkan wani al’amari da ya shafi saɓa wa ƙa’idar aiki daga ɓangaren jami’anta ta lambobin rassa kamar haka: “ACP X-SQUAD – 08034448617, PPRO – 08060545670, CRU – 08037681026 and PCB – 09016146804”.
